Saura Kiris Ya Sauka Daga Kujerar Mulki, Gwamnan Ribas Wike Ya Maida Adadin Hadimansa Zuwa 50,000

Saura Kiris Ya Sauka Daga Kujerar Mulki, Gwamnan Ribas Wike Ya Maida Adadin Hadimansa Zuwa 50,000

  • Gwamnan jihar Ribas ya kara zuwa da sabon salo yayin da ya nada sabbin hadimai da za su bashi shawari kan harkokin siyasa
  • Gwamnan ya bayyana cewa, ya cika dukkan alkawuran da ya daukar ma mutanen jiharsa, don haka zai kawo sauyi a yanzu
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP

Jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya sake daga adadin nade-naden hadimansa a fannin siyasa daga 28,000 zuwa 50,000, The Nation ta ruwato.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan ke bayyana cika dukkan alkawuransa na ayyukan ganin da ido tare da matsawa zuwa gina jama'a a fannin siyasar jihar tasa.

Gwamna Wike ya sake daga adadin hadimansa zuwa 50,000
Saura Kiris Ya Sauya Daga Kujerar Mulki, Gwamnan Ribas Wike Ya Maida Adadin Hadimansa Zuwa 50,000 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya ce wadannan ande-nade za su fara aiki ne nan take, haka nan Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yau Zan Kara Adadin Hadimaina Zuwa 100,000: Gwamna Nyesom Wike

Meye dalilin wadannan nade-nade barkatai?

A watan Maris din da ta gabata, gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta dukufa ne tare da maida hankali ga shirin walwala da karfafa jama'a wanda ya kira da 'stomach infrastructure'; zubi mai kama da siyasar cika ciki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wancan lokacin ya bayyana cewa, tunda gwamnatinsa ta cika dukkan alkawuran ayyukan gani da ido da ya dauka a jihar, to yanzu lokaci yayi da zai fara maida hankali ga diga romon dimokradiyya a bakunan wasu ta hanyar shirinsa na habaka fannin siyasa.

A cewarsa:

"Ganin yanzu mun yi kusan komai da muka yiwa al'ummar jihar Ribas alkawari, yanzu ne lokacin da za mu fara yin siyasar cika ciki."

An shiga jin dadi da annashuwa a jihar tun bayan da gwamnan ya samar da kari kan adadin hadimin da ya dauka a makon nan.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda masoya Nnamdi Kanu ke murna a cikin kotu bayan wanke shugaban IPOB

Hakan barazana ne ga tattalin arzikin Ribas, masanin tattalin arziki

Wani masanin tattalin arziki a jami'ar gwamnatin tarayya dake Kashere, Muhammad Shamsudden ya bayyana cewa, gwamna Wike na shirin wasa ne da kudin gwamnati wajen aikin da ba zai kari talakawan jiharsa ba.

Ya shaidawa wakilin Legit.ng Hausa cewa:

"Idan da gaske shawari zai saurara daga hadimai sama da 50,000, to ka fadamin, wanne shawari zai dauka cikinsu?
"Wannan kawai wata mafita yake son cimmawa, kuma ma hakan zai jawo kashe kudi ne babu wata dalili mai karfi.
"Kaddara zai basu albashin da jihohi ke ba masu ba da shawara, nawa ne zai kashe? Kuma wani ci gaba za su kawo? Wannan kada ka dauka wani abu ne mai amfani ko shigo da jama'a harkokinsa, kawai wata manufa ce a kar."

Ta kwabewa APC da Tinubu, mambobin APC 2000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, a ranar Laraba 12 ga watan Oktoba ne wasu mambobin APC akalla 2000 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ta dawa a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa: Inyamurai na da duk abin da ake bukata wajen mulkar Najeriya

A cewar mambobin da suka saki APC, ba za su ci gaba da zama a jam'iyyar da Buhari ya yi alkawari amma ya gaza cikawa ba, haka nan gwamnansu Mai Mala Buni.

Sabbin mambobin na jam'iyyar PDP sun kuma bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zabe mai zuwa, Rivers Mirror ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.