Sabuwar Rigima Ta Kunno, Jam'iyyar APC Ta Nesanta Kanta Da Wani Dan Takarar Gwamna a 2023
- Sabuwar rigima ta kunno kai a jam'iyyar APC reshen Abia kan sahihin dan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar
- Jam'iyyar APC da Abdullahi Adamu sun nesanta kansu daga zaben fidda gwanin da ya samar da tsohon ministan Buhari, Dr Uche Sampson Ogah
- Kwamitin NWC na jam'iyyar mai mulki yace shi dai Ikechi Emenike ya sani a matsayin dan takarar gwamnan jihar Abia
Abia - Jam'iyyar APC da shugabanta na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, sun nesanta kansu daga shirya zaben fidda gwanin da ya haifar da Dr Uche Sampson Ogah, a matsayin dan takarar gwamnan jihar Abia.
Sai dai kuma, kwamitin NWC ya ce zaben fidda gwanin da ya sani shine wanda ya samar da Ikechi Emenike a matsayin wanda ke rike da tutar jam’iyyar, Daily Trust ta rahoto.
Jam'iyyar da Adamu sun yi ikirarin ne a gaban wata babbar kotun tarayya ta hannun lauyansu, Farfesa Sam Eruogo (SAN).
Erugo ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar da Ogah ya shigar kan rashin hurumin kalubalantar zaben fidda gwanin da aka gudanar bisa doka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lauyan ya fada ma kotu cewa dokar Najeriya bata san da zaben fidda gwanin da Ogah ke ikirari a kai ba domin wani tsagi na jam'iyyar reshen jihar Abia ce ta gudanar da shi, rahoton Daily Post.
Ya ce Emenike ya lashe gudunma 184 na jihar sabanin na bangaren Uche wanda aka gudanar a waje guda.
Hakazalika, lauyan Emenike, Lateef Fagbemi(SAN), ya bukaci kotu da tatabbatar da wanda yake karewa bisa hujjar cewa shine ya yi nasara a zaben fidda gwani da kwamitin NWC na APC ya gudanar bisa doka.
Amma lauyan Ogah, Solomon Umoh (SAN), ya bukaci kotu da ta tilastawa APC gabatarwa INEC da sunansa a matsayin dan takara na hakika.
Umoh ya ce jami'an INEC sun sanya ido kan zaben fidda gwani na wakilai da ya samar da wanda yake karewa kuma cewa hukumar zaben ta gabatar da wani rahoto kan haka.
Bayan ta saurari bangarorin, Justis Bibta Nyako ta saka ranar 11 ga watan Nuwamba don sauraron shari'ar.
Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2
A wani labari na daban, darakta janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Aminu Tambuwal, ya ce jam’iyyarsa ta fi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sau dubu.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Tambuwal, wanda shine gwamnan jihar Sokoto ya yi bayanin dalilin da yasa PDP ce jam’iyyar da tafi dacewa da zama zabin yan Najeriya a babban zaben 2023 mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa yayin da PDP ta nuna adalci a tikitinta na takarar shugaban kasa, sam tikitin APC bai nuna dabi’ar tarayya ta Najeriya ba.
Asali: Legit.ng