An Kori Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasan ADC Daga Jam'iyya Ana Tsaka da Shirin Zaben 2023
- Watanni kadan gabanin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa ya rasa tikitin jam'iyyarsa saboda wasu dalilai
- Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC ya gamu da cikas a tafiyarsa yayin da jam'iyyar ta bayyana korarsa a hukumance
- An zargi dan takarar da aiki wajen dakile burin jam'iyyar tare da zarginsa da shirin siyar da tikitinta ga manyan jam'iyyu
Kaduna - Jam'iyyar ADC ta sanar da korar dan takararta na shugaban kasa Dumebi Kachikwu da abokin takararsa, Ahmed Rufai a hukumance yayin da ake ci gaba da shirin zaben shugaban kasa na 2023.
Jam'iyyar ta bayyana korar Kachikwu da abokin takararsa ne a wani taron gangami na musamman da ya gudana a yau Laraba 12 ga watan Oktoba a jihar Kaduna, Channels Tv ta ruwaito.
Hotuna: Kwankwaso Ya Kaddamar Da Ofishin NNPP A Lagos, Ya Ce Jam'iyyar 'Ta Yi Karfi Tamkar APC Da PDP'
Legit.ng Hausa ta tattaro wasu mambobi daban da jam'iyyar ta ADC ta kora duk dai saboda barkewar rikicin cikin gida gabanin zaben 2023.
Ga su kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Shugaban kwamaitin amintattu na ADC, Patricia Akwashiki
- Mataimakin shugaban jam'iyyar a yankin Arewa maso Gabas
- Wasu shugabannin jam'iyyar a matakin jiha
- Wasu jiga-jigan masu rike da mukamai a jam'iyyar
Me yasa aka kori dan takarar?
A cewar jam'iyyar ADC, ta kori Kachikwu ne saboda gaza kawo jerin abubuwan da yake son cimmawa idan ya gaji Buhari a 2023.
Jam'iyyar ta koka da hakan saboda tunda ya lashe zaben fidda gwani bata sake jin wasu manufofinsa ba.
Hakazalika, jam'iyyar ta kuma zarge shi da cin dunduniyar jam'iyyar, inda suka ce yana son hada kai da manyan jam'iyyu gabanin zaben badi.
Duk da korarsa, Legit.ng Hausa ta gano cewa, akwai sunansa a cikin jerin 'yan takarar da za su gwabza a zaben badi, kuma a jam'iyyar ta ADC.
Matsalolin Najeriya Sun Fi Karfin Tsoho Dan Shekara 70, Inji Matashin Dan Takara
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Accord Farfesa Chris Imulomen ya bayyana cewa, kalubalen da Najeriya ke fuskanta sun fi karfin shugaba mai shekarun da suka 70 wajen warware su, rahoton jaridar The Guardian.
A cewar farfesan, Najeriya na bukatar matashi mai jini a jika dake kan ganiyar kuruciya domin ba da jininsa wajen nemo mafita ga kasar.
Ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da jam'iyyarsu ta gudanar a jihar Kano, inda yace babbar matsalar Najeriya rarrabuwar kai ne.
Asali: Legit.ng