Ta kwabewa APC da Tinubu, mambobin APC 2000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Ta kwabewa APC da Tinubu, mambobin APC 2000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

  • Abubuwa na kara rincabewa a jam'iyyar APC a cikin 'yan lokutan nan yayin da ake tunkarar zaben 2023
  • A wannan karon, dubban mambobi ne suka sauya sheka daga jam'iyyar ta APC zuwa ta adawa a jihar Yobe
  • Wannan lamari dai na iya jawo cikas ga nasarar jam'iyyar a zabe mai zuwa kasancewar jam'iyyar na son ci gaba da mulki

Jihar Yobe - A ranar Laraba 12 ga watan Oktoba ne wasu mambobin APC akalla 2000 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ta dawa a jihar Yobe.

A cewar mambobin da suka saki APC, ba za su ci gaba da zama a jam'iyyar da Buhari ya yi alkawari amma ya gaza cikawa ba, haka nan gwamnansu Mai Mala Buni.

'Yan APC da dama sun koma PDP a jihar Yobe
Ta kwabewa APC da Tinubu, mambobin APC 2000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP | Hoto: Rivers Mirror
Asali: Facebook

Sun bayyana mubaya'arsu ga Atiku

Sabbin mambobin na jam'iyyar PDP sun kuma bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zabe mai zuwa, Rivers Mirror ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Akwai Adalci a PDP Sabanin APC: Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Bambancin Manyan Jam’iyyun Siyasar Kasar 2

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugabannin Kungiyar Magoya Bayan PDP ta Sokoto Sun Koma APC

Shugabannin kungiyar goyon bayan jam'iyyar PDP mai suna Ubandoma/Sagir Network a jihar Sokoto tare da daruruwan mambobinsu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Wannan batu na sauya sheka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Sanata Aliyu Wammako, kan harkokin yada labarai Malam Bashar Abubakar ya fitar a jihar ta Sokoto.

Aliyu Wammako ne sanata mai wakiltar mazabar Sokoto ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya.

A cewar Abubakar, kungiyar na kunshe ne da magoya bayan dan takarar gwamnan PDP, Malam Sa'idu Ubandoma da abokin takararsa, Alhaji Sagir Bafarawa, The Nation ta ruwaito.

Najeriya Ba Za Ta Tsira Ba Idan Aka Zabi Shugaba Kamar Buhari a 2023, Inji Dattijon Arewa

A wani labarin, mai magana da yawun majalisar dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmad ya bayyana cewa, bai dace Najeriya ta samu shugaba mai irin halayen Buhari ba, kuma dole shugaban Najeriya na gaba ya sha bamban da akidun Buhari.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a PDP yayin da shugabannin magoya baya suka sauya sheka zuwa APC a Sokoto

Baba-Ahmad ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa da jaridar Punch da aka buga a ranar Lahadi 9 ga watan Oktoba.

Da yake koka yadda mulkin Buhari ya kasance, Baba-Ahmad ya ce: “Bana tunanin za mu tsira na tsawon shekaru goma tare idan muka ci gaba da tafiya yadda muke a karkashin Buhari."

Asali: Legit.ng

Online view pixel