Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal

Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal

Gabanin babban zaben shekarar 2023, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar da jerin sunaye na karshe ne yan takarar shugaban kasa.

A cewar jerin sunayen, jam'iyyun siyasa 18 ne za su fafata a babban zaben da ake shirin yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.

Princess da Kachikwu
Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasa Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE. Hoto: Photo credits: Skywardnews Media-alert, Dumebi Kachikwu.
Asali: Facebook

Daga cikin yan takarar 18, guda biyu sun yi rajista da shaidar kammala makarantar frimare (FLSC) da ta kammala sakandare wato WAEC/SSCE, yayin da sauran suka yi rajista da HND, B.Sc da wasu manyan digiri, ciki har da MSc da PhD.

Legit.ng ta lura cewa yin rajista da kananan digiri ba ya nufin wani ya fi wani idan har dai digirin na cikin wadanda kundin tsarin mulki ta amince da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya

Kafin a zabi mutum matsayin shugaban kasa a Najeriya, kundin tsarin mulki na 1999, sashi na 131, ya ce dole dan takarar ya yi karatu zuwa a kalla matakin kammala frimare.

2023: Wane sharruda ake bukatan cika wa kafin a iya zaben mutum matsayin shugban Najeriya?

Ga abubuwan da doka ta buka mutum ya cika kafin zama shugaban kasar Najeriya bisa, kundin tsarin mulki

  • Ya kasance haifafan dan Najeriya ne
  • Ya kasance ya kai shekaru a kalla 35;
  • Ya zama mamba na jam'iyyar siyasa kuma jam'iyyar na daukan nauyinsa; kuma
  • Ya yi karatu zuwa a kalla matakin satifiket ko abin da ya yi dai-dai da shi.

1. Kachikwu Dumebi

Kachikwu Dumebi shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress, (ADC).

Dan shekara 48 ya mika takardar FLSC da WAEC a matsayin takardun karatunsa.

2. Nnadi Charles Osita

Nnadi Charles Osita shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Peoples Party, (APP).

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekaru 70 ba zai iya magance matsalolin Najeriya ba, inji mai son gaje Buhari

3. Ojei Princess Chichi

Ojei Princess Chichi ita ce yar takarar shugaban kasa na jam'iyyar Allied Peoples Movement, (APM).

Chichi ce yar takarar shugaban kasa mace tilo a zaben. Ta mika takardar kammala sakandare a daga makarantar American International a Switzerland.

A lura cewa wasu yan takarar suna da manyan takardun karatu amma saboda dalilan da su kadai suka sani, suka zabi su mika FSLC, NECO da WAEC tunda doka ta amince da hakan.

Yan takarar mataimakan shugaban kasa da suka mika SSCE kawai

1. Kyabo Yahaya Muhammad

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar National Rescue Movement, NRM.

FSLC da SSCE ya mika a cewar jerin sunayen da INEC ta fitar.

2. Johnson Emmanuel Chukwuka

Shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance, AA. WAEC ya mika wa INEC.

3. Zego Haro Haruna

Zego shine mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PRP.

FSLC da WAEC ya mika wa INEC.

Kara karanta wannan

2015: Daga neman canji, 'yan Najeriya suka zabi Buhari; yunwa, fatara da rashin tsaro

4. Buhari Muhammad Ahmed

Buhari Muhammad Ahmed shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC.

FSLC da WAEC ya mika wa INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel