Sanatan Kano Ya Bayyana Wanda Zai Yi Nasara a 2023, Yace Ba a Maganar NNPP

Sanatan Kano Ya Bayyana Wanda Zai Yi Nasara a 2023, Yace Ba a Maganar NNPP

  • Kabiru Ibrahim Gaya yace jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ba za tayi galaba a Kano ba
  • Sanata Kabiru Gaya yana ganin tasowar NNPP ba za ta kawowa jam'iyya mai mulki wani cikas ba
  • ‘Dan majalisar na Kudancin jihar Kano yana sa ran doke Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila a 2023

Kano - Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kudancin Kano a majalisar dattawa yace jam’iyyar hamayya ta NNPP ba za ta kawowa APC barazana ba.

The Cable ta kawo rahoto cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a gidansa da ke garin Kano.

“A Kano, muna da jam’iyyu biyu ne – APC sai kuma PDP. Jam’iyyar PDP ta rabu biyu, ‘Yan Kwankwassiyya sun kafa NNPP.
Har yanzu APC da PDP kadai muke da su a Kano. Saboda haka ina sa ran jam’iyyar APC za ta yi nasara a Kano a zaben 2023.”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Zata Ba Mutane Mamaki a Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Kwankwaso

- Kabiru Ibrahim Gaya

Barazanar Kawu Sumaila

An rahoto Sanatan yana cewa babu shakka babban abokin adawarsa a zaben Sanatan Kano ta Kudu, Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila yana tara jama’a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gaya wanda ya dade a majalisar dattawa yake cewa wannan ba zai hana shi galaba a kan Hon. Sumaila da jam’iyyar NNPP ba domin ya fi shi yawan magoya baya.

'Dan takaran Sanatan Kano a NNPP
Mutanen Abdulrahman Kawu Sumaila Hoto: @Kawu_Sumaila_1
Asali: Twitter
“Kawu Sumaila yana kokari sosai, amma na fi shi mutane, nayi imani zan lashe zaben.”

- Kabiru Ibrahim Gaya

Hon. Sumaila tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya ne wanda ya yi aiki a fadar shugaban kasa a matsayin mai ba shugaba Muhammadu Buhari shawara.

Daga baya fitaccen ‘dan siyasar ya bar jam’iyyar APC zuwa NNPP da ta ba shi takarar Sanata.

Gaya: A daina sayen kuri'u a zabe

Gaya ya yi kira ga ‘yan siyasa su kula da jin dadin al’ummarsu, su daina sayen kuri’u. Sanatan yace sabuwar dokar zaben 2022 za ta hana mutane suyi magudi.

Kara karanta wannan

Allah Ya Wadarar A Sake Baiwa PDP Amanar Baitul Malin Al'umma, Lai Mohammed

‘Dan siyasar yace bai amfani da kudi wajen lashe zabe, sai dai ya yi wa mutanen mazabarsa ayyukan da za su ji dadi kamar gina makarantu da hanyoyi.

Za mu tallafawa matasa - NNPP

A baya an ji labari Rabiu Musa Kwankwaso yace gwamnatin NNPP za ta bunkasa harkar ilmi a kasar nan, kuma zai dage wajen inganta rayuwar matasa.

Da yake jawabi a wajen bude ofishin yakin neman zaben NNPP a jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana inda zai sa gaba idan NNP ta lashe zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel