2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya

2023: Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da Naira 10, In Ji Dan Takarar Shugaban Kasa Daga Arewacin Najeriya

  • Hamza Al-Mustapha, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance ya ce bai taba satar ko da naira 10 ba daga baitul malin Najeriya a rayuwarsa
  • Tsohon babban dogarin na marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ak yi da shi
  • Al-Mustapha ya yi ikirarin cewa masu son ganin bayansa suna son su wawushe kudaden da Abacha ya bari ne amma a yanzu ya yafe musu daurin da suka yi masa

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance (AA), Hamza Al-Mustapha ya ce bai taba satar kudi ba ko daukan arzikin kasa, sai dai ya kare dukiyar kasar duk da matsin lamba da wasu suka yi masa.

Al-Mustapha, yayin hira da aka yi da shi a shirin Politcal Paradigm na Channels Television a ranar Talata ya ce:

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ba Ta Da Halastacen Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Ku Zabi Atiku, PDP Ga Yan Najeriya

Al Mustapha
Ban Taba Satar Ko Sisi Ba, Daidai Da N10, In Ji Al-Mustapha. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ban da kudi, ban taba satar ko da naira 10 ba. Na kallubalanci gwamnatoci biyu; Na kallubalanci gwamnatin Abdulsalami Abubakar, kuma na kallubalanci gwamnatin (Olusegun) Obasanjo. Sun yi bincike.
"Manyan hukumomin bincike na kasa da kasa (yan sanda) sun yi bincike a kai na. An dauki hoton ido na da zanen hannu a duk duniya amma ba a ga komai ba. A maimakon su fada wa duniya cewa ban aikata komai ba, sun ajiye abin a gefe.

Al Mustapha ne babban dogarin tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha daga 1993 zuwa 1998.

Kudin Abacha suke son su kwashe shi yasa suke son kashe ni - Al-Mustapha

A cewarsa, wadanda suka zarge shi da kisa, yunkurin juyin mulki, safarar miyagun kwayoyi da almundaha da kudade 'ba su kyauta ba' amma ya yafe musu.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba Goodluck ne alherin da Najeriya ta taba gani a tarihi, inji gwamnan Arewa

Ya ce:

"Na yi fuskanci alkalai 14 cikin shekaru 15 kuma duk ba a same ni da laifi ba."

Ya ce wadanda ke nufinsa da sharri sun so daukan ransa bisa doka da akasin hakan domin suna son kwashe kudaden Abacha idan sun hau mulki.

Dan takarar shugaban kasar na AA ya ce:

"Me yasa suke son su kashe ni? Kawai saboda abin da na sani ne. Na tsinci kaina a wani hali da na ki cin amanar Najeriya hakan ya jefa ni cikin matsala."

Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya

A wani rahoton, Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha ya jadada kudirinsa na zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023

Al-Mustapha, wanda shine dan takarar shugaban jam'iyyar Action Alliance, AA, a zaben 2023 ya ce a shirye ya ke "ya sadaukar da rayuwarsa don Najeriya da walwalar yan Najeriya".

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a yayin hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164