Amaechi, da ‘Yan APC 10 da Suka Nemi Takaran 2023, Amma Aka Daina Jin Duriyarsu
- Wasu a cikin wadanda suka nemi zama ‘yan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC sun yi kusufi
- Tun da aka ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne zai yi wa APC takara, aka rasa inda suka shige a siyasa
- A wannan jeri akwai Sanatoci, tsofaffin shugabannin majalisar tarayya da wasu tsofaffin Gwamnoni
FCT, Abuja – A watan Yunin 2022 aka san wanda zai rikewa jam’iyyar APC mai mulki tuta a zaben shugabancin Najeriya da za ayi a farkon 2023.
Samun nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya jawo an daina jin inda sauran abokan hamayyarsa a zaben fitar da gwanin jam’iyyar APC suka shiga.
Legit.ng ta tattaro manema takara a APC da suka yi barci:
1. Dimeji Bankole
Rt. Hon. Oladimeji Bankole ya yi takara da Bola Tinubu amma bai kai labari ba. Tun da aka gama zabe, aka daina jin motsin tsohon shugaban majalisar tarayyar.
2. Tein Jack-Rich
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tein Jack-Rich fitaccen attajiri ne mai shekara 48 a Duniya. ‘Dan siyasar yana cikin wadanda ya rasa tikitin takarar shugaban kasa, sai aka daina jin duriyarsa.
3. Rochas Okorocha
Rochas Okorocha yana cikin wadanda suka ji kunya a zaben fitar da gwanin shugaban kasa a APC domin bai tashi da kuri’a ko daya ba, har yanzu ya yi tsit.
4. Tunde Bakare
Tunde Bakare ya yi suna ne bayan zamansa abokin takarar Muhammadu Buhari a CPC a 2011. Bakare yana cikin wadanda ake cigiya yau a manyan ‘ya 'yan APC.
5. Emeka Nwajiuba
Emeke Nwajiuba ne ya fara ayyana niyar tsayawa takarar shugaban kasa, bayan ya sha kashi ba a sake jinsa ba, sai da ya kai karan ‘yan takaran APC da PDP a kotu.
6. Ajayi Boroffice
Sanatan Ondo, Ajayi Boroffice yana cikin wadanda suka janyewa Bola Tinubu, daga lokacin aka daina maganarsa. Babu mamaki ya taka rawar gani a wajen kamfe.
7. Ken Nnamani
Sanata Ken Nnamani ya nemi tikitin jam’iyyar APC amma bai yi nasara ba. Tsohon shugaban majalisar dattawan yana cikin wadanda ba a maganarsu a yanzu.
8. Ogbonnaya Onu
Jerin yana dauke da Ogbonnaya Onu wanda ya ajiye mukaminsa a gwamnati. Tsohon gwamnan ya fadi babu girma a zaben tsaida gwani, ana neman rufe babinsa.
9. Ikeobasi Mokelu
‘Dan takaran da ya fi kowa tsufa a zaben tsaida ‘dan takaran APC shi ne Ikeobasi Mokelu. Kafin zaben an manta da shi a siyasa, da alama dai ya koma gidan jiya.
10. Ahmad Sani Yariman Bakura
Tun 2007 Ahmad Sani Yariman Bakura yake neman shugabanci, a wannan karo ma bai yi nasara ba. Sanatan bai samu tikitin APC ba kuma ba zai koma majalisa ba.
Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023
11. Rotimi Amaechi
Legit.ng Hausa ta kara da Rotimi Amaechi wanda ya yi biyu-babu da ya ajiye mukaminsa. 'Dan siyasar ya yi shiru yayin da yaransa a siyasa suke ta barin APC.
Ana adawa da Tinubu-Kashim
Dazu kun ji labari cewa Kiristocin da ke APC sun yi zama da tsofaffin gwamnoni da manyan ‘yan siyasan da suka fito daga jihohin yankin Arewacin Najeriya.
A karshen taron da aka yi, an amince cewa mabiya addinin kirista na jam’iyya mai mulki za su goyi bayan wani ‘dan takaran shugaban kasa dabam a 2023.
Asali: Legit.ng