Allah Ne Ya Turo Tinubu Ya Cece Mu, Jigon APC Ya Hango Alherin Dan Takararsu

Allah Ne Ya Turo Tinubu Ya Cece Mu, Jigon APC Ya Hango Alherin Dan Takararsu

  • Gabanin zaben 2023, jigo kuma matashin dan jam'iyyar APC, Obidike Chukwuebuka ya ce dan takarar shugaban kasansu zai kawo sauyi a Najeriya
  • Obidike, wanda shine darakta janar tawagar gangamin nuna goyon bayan APC ya ce, tsohon gwamnan na Legas shine mai ceton 'yan kasar nan
  • Jigon na APC ya kuma yi tsokaci ga irin ayyukan da Tinubu zai yi a fannin wutar lantarki, ilimi, lafiya, man fetur da dai sauransu

Obidike Chukwuebuka, mamba a jam'yyar APC ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, zaben 2023 mai zuwa zai zo da sauyi mai yawa idan aka zabi Asiwaju Bola Tinubu.

Obidike, wanda kuma shine darakta janar na tawagar gangamin nuna goyon bayan APC ya bayyana wannan batun ne a jiya Alhamis 6 ga watan Oktoba, kamar yadda ya turowa Legit.ng a wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Cikakken Jawabin da 'Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi Daga Shigowa Najeriya

Bola Ahmad Tinubu ne zai ceto Najeriya, inji jigon APC
Allah Ne Ya Turo Tinubu Ya Cece Mu, Jigon APC Ya Hango Alherin Dan Takararsu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A cewarsa, Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC ne macecin da Allah ya turo ya tsamo Najeriya daga halin kakani-kayi.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Allah ya turo mai cetonmu (Tinubu) don ya sake gina Najeriya. Da yawa basu yi imani da Annabi Isah ba har sai da ya fara nuna mu'ijiza. Allah ne ya zabi Asiwaju ya jagorance mu ga tsira."

Ya kuma bayyana cewa, idan 'yan Najeriya suka ba Tinubu dama, zai kawo sauyi ta fannin tattalin arziki, domin kuwa zai gaggauta kawo mafita a fannin.

A bangare guda, ya ce Tinubu zai tabbatar da gabaka wutar lantarki a Najeriya, inda zai mai da kasar ta zama akwai wuta a ko'ina 24/7.

Meye Tinubu zai yi a fannin man fetur?

Obidike ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, idan aka zabi Tinubu zai kawo tsarin da zai habaka wutar lantarki ta hanyar tsarin adana man fetur don amfanin kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

A cewarsa, tsarin da Tinubu zai kawo zai ba da mafita ga tsadar man fetur da kasar nan ke fuskanta a yanzu.

Ya kara da cewa, Tinubu zai hada kai da 'yan kasuwa masu zaman kansu domin gayyato masu zuba hannayen jari daga kasashen waje don habaka fannin kasuwanci da rage zaman banza.

Hakazalika, ya ce Tinubu zai tabbatar da kawo kashen yajin aikin jami'o'i, domin kuwa zai kawo tsarukan da za su karfafa ma'aikatan jami'a.

Diyar Atiku Za Ta Jagoranci Majalisar Kamfen Din Matasan PDP Gabanin 2023

A wani labarin, daidai da shirin kwamitin dabaru na kasa (NSC) na PDP, jam'iyyar ta kaddamar da majalisar kamfen din matasa da ta kira NYCC don cimma burin gaje Buhari a zaben 2023.

Majalisar kamfen din jam'iyyar PDP na da burin tabbatar dukkan 'yan takarar PDP sun lashe zabe a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Dan takarar gwamnan APC a Kaduna ya fadi dan takarar shugaban kasan da ya fi cancanta a zaba

Legit.ng ta tattaro cewa, majalisar ta NYCC za ta dukufa ne gadan-gadan wajen tattarawa da samo kuri'un matasa maza da mata a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.