Daga Karshe, An Faɗi Halin da Tinubu Ke Ciki da Muhimmin Abinda Ya Kai Shi Landan

Daga Karshe, An Faɗi Halin da Tinubu Ke Ciki da Muhimmin Abinda Ya Kai Shi Landan

  • Jam'iyyar APC reshen ƙasar Burtaniya ta karyata jita-jitar da mutane ke yaɗa wa cewa Tinubu ya je jinya ne a Landan
  • Shugaban tawagar kamfen APC na ƙasashen waje, Joseph Adebola, yace ɗan takarar nan nan cikin koshin lafiya
  • Yace tsohon gwamnan Legas ɗin na gudanar da wasu taruka da masu ruwa da tsaki gabanin fara kamfen 2023

Jam'iyyar APC reshen ƙasar Birtaniya tace ɗan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na nan cikin ƙoshin lafiya saɓanin jita-jitar da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta.

Mista Joseph Adebola, shugaban tawagar yaƙin neman zaɓen APC ta Burtaniya (UK), shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Obi Ɗan-Gata: Gwamnoni 18 Ne Ke Marawa Obi Baya, Ohanaeze

Asuwaju Bola Ahemd Tinubu.
Daga Karshe, An Faɗi Halin da Tinubu Ke Ciki da Muhimmin Abinda Ya Kai Shi Landan Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yace raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa Tinubu na fama da rashin lafiya kuma ya garzaya ƙasar waje ne domin neman magani ba gaskiya bane, jaridar Vanguard ta ruwaito.

"Bisa rashin sa'arsu, mummunan tunanin da suke a kan Tinubu ba zai zo ya wuce ba saboda ba su ne Allah ba, mai ba da rayuwa," inji shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Me Ya kai Bola Tinubu Landan?

"Abin da muka sani, Tinubu na gudanar da tarukan dabaru da masu ruwa da tsaki a nan UK, ɗaya daga cikin irin waɗan nan tarukan, Tinubu ya gana da mambobin tawagar kamfe ɗinsa."
"Tawagar ta ƙunshi Alhaji Ibrahim Masari, Sanata Tokunbo Afikuyomi, mataimakin Daraktan kwamitin shirye-shirye na PCC da wasu ƙusoshi a siyasa nan a UK."

- Joseph Adebola

Ya ƙara da cewa taron ya maida hankali ne wajen ɗaukar matakin shawo kan matsaloli gabanin fara yaƙin neman zaɓe. Yace bayan kammala taron an ɗauki hoto a wurin.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal Ya Faɗi Rana Da Jihar da PDP Zata Fara Yaƙin Neman Zaɓen Atiku 2023

"Ɗaya daga cikin Hotunan da suka karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna Tinubu na tafiya don koma wa gida daga lambu. Kuma taron ya nuna cewa ɗan takarar ba zaune yake ba."

Bugu da ƙari ya tabbatar da cewa tawagar Kamfen APC-UK na aiki ba dare ba rana wajen haɗa kan 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje su koma gida don mara wa Tinubu baya a 2023.

A wani labarin kuma Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace idan har gwamnoni suka zare hannunsu jam'iyyar ba zata kai labari ba a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa yace nasarar APC na hannun Allah kuma tana hannun gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel