Obi Ɗan-Gata: Gwamnoni 18 Ne Ke Marawa Obi Baya, Ohanaeze

Obi Ɗan-Gata: Gwamnoni 18 Ne Ke Marawa Obi Baya, Ohanaeze

  • Peter Obi dai shine ɗan takara ɗaya tilo da ya fito daga kabilar igbo da kungiyar Ohanaeze ke goyon baya
  • Ohanaeze Ndigbo tace Peter Obi ne zai lashe zaben shugaban kasa a Febrairun 2023
  • Ana ganin dai farin jini Obi yafi karfi ne a tsakanin matasan da ke amfani da ƙafafe sada zumunta

A jiya laraba ne ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, ta yi ikirarin cewa gwamnoni 18 masu ci da kuma wasu tsofaffin shugabannin kasar nan ne ke goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abakaliki, wadda jaridar "The Guardian" ta samu, ta hannun babban sakataren kungiyar al’ummar Igbo'n, Okechukwu Isiguzoro, wadda ta bayyana "cewa gwamnonin da suke a jam'iyu dabam-daban sun nuna goyon bayansu ga Obi, inda ya kara da cewa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bayan Shafe Watanni Uku, Yan Bindiga SUn Saki DPOn Yan Sandan Da Suka Sace

Tuni dai jam’iyyun APC da PDP da sauran jam’iyyun siyasa suka fara fargabar da ganin irin wannan ci gaban a yaƙin neman zaɓen Obi'n.

Ƙungiyar Ohanaeze, ta ya yaba da jajircewa da ‘yan Najeriya suka yi, waɗanda suke sassa daban-daban na ƙasar nan kan irin goyon bayansu ga Obi, ta kuma bukaci da ƴan ƙasar ci gaba da dagewa, tana mai cewa "wannan yunkuri ne na kwato Najeriya daga zamanin masu babaƙere da masu hadama daga cikin ƴan siyasar ƙasar.

A cewar Isiguzoro, gangamin nuna bayan Obi mai taken "Obi-dients" da aka gudanar a fadin kasar nan, ya sanya dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da sauran ƴan takara cikin tsaka mai wuya, sakamakon yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ke kara karɓuwa, musamman a lokutan bukukuwan ƴan cin kai da aka gudanar a faɗin kasar.

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

Daga Karshe, An Faɗi Gaskiyar Halin da Bola Tinubu Ke Ciki Da Babban Abinda Yake Yi a Landan

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan yunkuri ne na ceto kasar nan daga halin ƙunci, koma bayan tattalin arziki, yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), rashin tsaro da cin hanci da rashawa.
“Ya zuwa yanzu, ‘yan Najeriya sun nuna a shirye suke su dawo da martabar ƙasarsu ta hanyar dangwala ƙuri'a, wanda hukumar zabe ta kasa (INEC) zata shirya haɗi da gudanarwa.
“Yayin da muke magana, kimanin gwamnoni 18 daga Arewa da Kudu, na jam’iyu dabam-daban ne suke suna nuna goyan bayansu a bayan fage tare da shiryawa Obi hanyoyin lashe zaben shugaban kasa a 2023.
“Bugu da kari, tsofaffin shugabannin kasa da dattawa daga jihohi dabam-dabam suma suna goyon bayan takarar Obi.

A wani ci gaban ɗan takarar gwamnan jihar Ebonyi na jam’iyyar LP, Edward Nkwegu, yayi ƙira da jami'an tsaro, da su sake dage damtse dan ganin anyi zaɓen lafiya, ya bayyana hakan a filin jirgin saman Akanu Ibiam, na jihar Enugu, jim kaɗan bayan saukarsa ya ce "ƴan Najeriya sun shirya maida martabar ƙasar ta hanyar amfani da zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel