Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Ranar Fara Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Ranar Fara Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa Na 2023

  • Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP tace ta kammala shiri tsaf domin fara tallata yan takararta ga yan Najeriya
  • Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato yace PDP zata fara kamfen daga Uyo, babban birnin Akwa Ibom ranar Litinin
  • Tambuwal yace saɓanin da aka samu tsakanin ƙusoshin PDP zai zama tahiri nan ba da jima wa ba

Abuja - Jam'iyyar hamayya Peoples Democratic Party (PDP) tace ta kammala duk wasu shirye-shiryen domin fara yaƙin neman zaɓe na shekarar 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan duba Ofishin kamfen Atiku Abubakar da ke Abuja, Darakta Janar na kwamitin kamfen shugaban ƙasa a PDP, Aminu Tambuwal, yace zasu fara kamfe a Uyo, babban birnin Akwa Ibom ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Muhimmin Abun Da Zan Yi Idan Na Ɗare Kujerar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 2023, Kwankwaso

Tutar jam'iyyar PDP.
Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Ranar Fara Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan jihar Sakkwaton yace jam'iyyar PDP ce kaɗai ta kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓenta, ya ƙalubalanci sauran jam'iyyu da cewa ba su shirya wa kamfe ba.

Tambuwal ya ƙara da cewa har yanzu PDP ce jam'iyya mai nasara a kafatanin sassan ƙasar nan kuma har da kudu maso gabas, saɓanin yadda ake yaɗa cewa ta rasa ƙarfinta a yankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ruwayar Tribune, Gwamna Tambuwal yace:

"Da izinin Allah, zamu fara yaƙin neman zaɓe ranar Litinin mai zuwa a Uyo, jihar Akwa Ibom. An kammala dukkanin wasu shirye-shirye tsaf domin tabbatar da taro ya tashi lafiya."
"Kamfem mu zai kasance kan batutuwa masu muhimmanci. Zamu tallata 'yan takarar mu bisa abubuwan da suka fito a zahirance, waɗanda muke ganin sune hanyar maslaha."

Rikicin jam'iyyar PDP

Da yake tsokaci game da rikicin da ya addabi PDP, gwamnan yace, "Saɓani ne ma siyasa kuma muna aiki ba dare ba rana domin warware baki ɗaya matsalolin."

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Mutu Murus Babu Sauran Burbushinta a Jihata, Inji Wani Gwamna APC

"Mun shirya tsaf domin zuwa shiyyar kudu maso gabas kuma muna da yaƙinn mu ne zaɓi na lamba daya a kudu maso gabas. Sanan kuma zamu karaɗe ko ina a shiyyoyi shida na ƙasar nan."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Jam’iyyar APC ta sanar da cewa za ta fara gudanar da harkokin kamfen dinta na shugaban kasa na 2023 a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba.

Jam’iyyar mai mulki ta sanar da hakan ne duk da cewar dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, yana chan a birnin Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel