Mata Sun Fito Kwansu da Kwarkwata Domin Nuna Goyon Bayan Tinubu a Jihar Imo

Mata Sun Fito Kwansu da Kwarkwata Domin Nuna Goyon Bayan Tinubu a Jihar Imo

  • Mata sun yi dandazo a jihar Imo domin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC
  • Bola Ahmad Tinubu ne dan takarar shugaban kasa da APC ta tsayar, kuma tuni aka fara tallata shi a Najeriya
  • Gwamna Uzodinma na Imo ya bayyana kwarin gwiwar cewa, Tinubu ne ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari

Owerri, jihar Imo - Dandazon mata da dama daga yankin su Peter Obi sun yi tururuwar nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasan jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

A gangamin da jaridar TheCable tace matan sun yi a jihar Imo ta Kudu maso Gabas, matan sun mamaye Hero Square dake Owerri kana suka gangara har zuwa cibiyar manyan taruka ta IICC duk dai a birnin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Matan Imo sun ce sai Tinubu
Mata Sun Fito Kwansu da Kwarkwata Domin Nuna Goyon Bayan Tinubu a Jihar Imo | Hoto: thecable.com
Asali: UGC

Da yake magana yayin da ya karbi dandazon matan, gwamna Hope Uzodinma na jihar ya bayyana jin dadinsa da irin kaunar da suke nunawa dan takarar na APC.

A cewar gwamnan:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A nan yankin Kudu maso Gabas, APC na da karfi. Muna nan a ko'ina a yankin; lungu da sako kuma muna nan kekam muna goyon bayan dan takararmu na shugaban kasa da mataimakinsa da ma sauran 'yan takarar APC."
"Tabbas muna farin ciki da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kuma muna farin ciki da jam'iyyarmu da dan takarar shugaban kasanmu da abokin takararsa."

Tinubu zai kawo sauyi, inji matar Uzodinma

A bangarenta, matar gwamnan jihar ta Imo, Chioma Uzodinma ta bayyana bayyana kwarin giwar cewa, Tinubu zai yi abin kirkir idan aka bashi dama a zaben 2023.

Ta kuma bayyana cewa, mijinta ya yi matukar kokari wajen sauya rayuwar mutane da dama a Imo, musamman ma mata, rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023

Daga nan ne ta kuma bayyana irin kwazon da Tinubu ya yi a lokacin da yake gwamna a Legas da kuma irin ci gaban da ya kawo a siyasar kasar nan.

'Yan IPOB Ba ’Yan Ta’adda Bane, Na Zauna da Su, Inji Peter Obi a 2017

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya taba kakabawa gwamnatin Najeriya laifi wajen ta'azzarar ayyukan barna daga 'yan awaren IPOB.

Ya kuma ga laifin gwamnati da ta ayyana kungiyar ta su Nnamdi Kanu a matsayin ta 'yan ta'adda, Premium Times ta ruwaito.

A ranar 1 ga watan Oktoban 2017 ne Peter Obi ya bayyana a gidan talabijin na Channels ya bayyana wadannan maganganu na ganin laifin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.