Yadda Gwamnoni Ke Taimakawa Wajen Tada Rikici a Lokutan Zabe, Bayanin Oshiomole
- Tsohon gwamnan jihar Edo ya bayyana bacin ransa da yadda wasu gwamnoni ke taimakawa wajen ta'azzarar tsaro a lokacin zabe
- Tsohon ministan ya ce tabbas wasu gwamnoni ne ke siyawa tsageru bindigogi AK-47 a duk lokacin da zabe ke kara karatowa
- Ana yawan samun tashe-tashen hankula a lokutan zabe a Najeriya, lamarin da ke sanya tsoro a zukatan 'yan kasa
Najeriya - Tsohon minsitan Buhari, kuma tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole ya bayyana yadda gwamnoni ke taimakawa wajen dagula kasar nan a lokutan zaben.
Oshiomole ya bayyana sirrin gwamnonin ne a wata tattaunawa da kungiyar YIAGA Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya da gidan talabijin na Channels.

Asali: UGC
Hakazalika, ya bayyana cewa, ya kamata jam'iyyun siyasa suke bayyanawa mabiyansu cewa, zabe lamari ne na 'yanci kuma damar bayyana ra'ayi.
Ya kara da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya kamata mu ke fadawa shugabanninmu cewa, dole su yi da'awar yin zabe ba tare da tashin hankali ba. Ina sake nanata cewa, dukkanmu aiki ne a kanmu. Najeriya ta fi gaban dukkan jam'iyyun siyasa."
Ba haka siddan ake samun makamai ba
Oshiomole ya bayyana cewa, yawancin makaman da ake gani a hannun masu dagula lamarin zabe ba abu ne mai sauki samunsu ba, Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon gwamnan na Edo ya ce:
"A lokacin da nake gwamna na fadi haka, ku tambayi (tsohon) shugaban kasa Goodluck Jonathan, na tada batu a wata ganawa a Villa cewa, wasu gwamnoni a wasu lokutan na taimakawa wajen tada hankali a lokacin zabe saboda AK-47 ba abu ne mai araha ba kamar kosai.
"Sannan duk lokacin da ka ga matasa maras sana'a dauke da makaman AK-47, waye ke samar dasu? Don haka shugabancin siyasa nauyi ne a ka, dole mu dauki wannan nauyin."
A bangare guda, ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa jajircewa wajen tabbatar an samu zaman lafiya da wataccen tsaro a Najeriya.
Ban Sani Ba Ko Tinubu Yana Najeriya, Inji Jigon Kamfen Din Tinubu, Oshiomole
A wani labarin, mataimakin daraktan gangamin kamfen din APC, Adams Oshiomole ya ce bai da masaniya ko dan takarar shugaban kasansu na nan a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 28 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.
Ya bayyana cewa:
"Ba da shi nake aiki kullum ba, ban san yana nan ko bai nan ba."
Asali: Legit.ng