Abin da ya sa Ake yi Mani Sharrin Satar $41.8m a lokacin ina Gwamna inji Sanata
- Ana yada labari cewa FBI ta gano Chimaroke Nnamani ya saci kudi a sa’ilin da yake Gwamna a Enugu
- Sanata Nnamani yace wannan ba aikin kowa ba ne illa ‘yan adawa da masu neman ci masa mutunci
- Tsohon Gwamnan yace albashinsa a shekara a lokacin da ya yi mulkin shekara takwas bai zarce $10,000 ba
Abuja - Chimaroke Nnamani ya musanya rade-radin zargin da ke yawo na cewa ya sace $41.8m daga asusun gwamnati lokacin yana gwamnan jihar Enugu.
Chimaroke Nnamani wanda yanzu Sanata ne mai wakiltar gabashin Enugu ya fitar da jawabi, yana mai karyata zargin. Premium Times ce ta kawo rahoton.
A wani jawabi na musamman da ya fitar a ranar Talatar nan, ‘dan siyasar yace labarin karya wasu ke yadawa a kan shi saboda ra’ayin siyasar da ya dauka.
Nnamani ya boye kudi a Amurka
Rahotanni na yawo cewa Chimaroke Nnamani ya yi awon-gaba da $41.8m daga cikin Baitul-mali, ya yi amfani da kudin wajen sayen kadarori a kasar Amurka.
Sanata Nnamani yana mai wanke kan shi, yake cewa a lokacin da ya rike kujerar gwamna tsakanin 1999 da 2007, albashin da yake karba a shekara $10,670 ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban ‘Dan siyasar yace ba zai yiwu mai tashi da fam $10,670 a tsawon shekara, ya iya mallakar kadarori masu tsada sosai a birnin Florida a wancan lokaci ba.
"Zan cigaba da magana, in addabe su. Na san matsayin da na dauka zai jawo mania suka daga wadanda ba su iya yarda wani ya ja da su.
Damukaradiyya ya bada damar ka fada-wani ma ya fada. Idan ba zan bayyana ra’ayi na, in dauki matsaya ba, to waye zai bayyana nasa?”
“Ba a taba yin wannan shari’a a ko ina ba.”
- Chimaroke Nnamani
Har ila yau, an rahoto jigon na jam’iyyar PDP yana cewa ya daura jiharsa ta Enugu a kan turba mai kyau a lokacin yana mulki, yace babu wanda zai ja da haka.
A karshe, Sanatan ya yi kira ga mutanen Najeriya su yi watsi da wannan rahoto da yace ‘yan adawa da kwararrun masu bata suna suke yada shi da sunan FBI.
Takarar Sangodara a Legas
Dazu an ji labari takarar Mosunmola Sangodara a APC tana fuskantar cikas yayin da aka shigar da ita kotu bisa zargin karyar takardar shaidar karatu.
Ana so a hana Hon. Sangodara mai wakiltar mazabar Surulere II a majalisar dokokin jihar Legas shiga zaben tazarce a 2023 saboda zargin badakalar nan.
Asali: Legit.ng