Princewill: Atiku da Peter Obi Za Su Iya Taimakawa Tinubu Ya Ci Zabe a Saukake

Princewill: Atiku da Peter Obi Za Su Iya Taimakawa Tinubu Ya Ci Zabe a Saukake

  • Prince Tonye Princewill yace akwai yiwuwar zaben 2023 ya je zagaye na biyu saboda abubuwan da ya hango
  • ‘Dan siyasa yace tsayawa takarar Peter Obi za ta nakasa kuri’un Atiku Abubakar a wasu yankin kudancin Najeriya
  • Princewill ya bar APC saboda ta tsaida Bola Tinubu/Kashim Shettima, amma yana so jam’iyyar tayi nasara a Ribas

Abuja - Tonye Princewill wanda na hannun daman Rotimi Amaechi ne, yana ganin da kamar wahala a iya cewa ga wanda zai lashe zaben shugaban kasa.

The Cable ta rahoto Tonye Princewill a ranar Litinin yana cewa kuri’un da za a raba tsakanin jam’iyyun PDP da LP za su taimakawa Bola Tinubu a 2023.

Princewill yana ganin ‘dan takaran jam’iyyar LP watau Peter Obi zai gwagwiye kuri’un da ya kamata a ce Atiku Abubakar mai takara a PDP ya samu.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

Amma dai zuwa yanzu, ‘dan siyasar yace ba za a iya hangen ‘dan takaran da za iyi galaba ba.

Yadda abin yake a yanzu - Princewill

“Idan muka duba lamarin da kyau a halin yanzu, ina ganin akwai yiwuwar zaben ya je ga zagaye na biyu, a yadda abubuwa suke.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma ya yi wuri a iya cewa hakan, kuma abubuwa da-dama za su iya canzawa ko kuma su ki canzawa – a nan da watanni biyar."

- Tonye Princewill

Atiku da Peter Obi
Atiku, Obi da Tinubu Hoto: www.icirnigeria.org
Asali: UGC

Sauya-sheka daga Jam'iyyar APC

Da aka yi hira da shi, Princewill yace ya bar jam’iyyar APC mai mulki ne saboda ta tsaida Musulmai biyu a matsayin ‘yan takaranta a zaben shugaban kasa.

"Na fito karara nayi bayani, ba na goyon bayan Musulmi-Musulmi a Aso Villa.
Amma idan ba mu bi a hankali ba, a maimakon Peter Obi ko Atiku su karbi mulki, za a jawo Tinubu ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Wanke Wanda Ake Zargi da Goyon Bayan Atiku a Fadar Shugaban kasa

Meyasa na fadi haka? PDP ta na da karfi ne a Kudu maso kudu, kudu maso gabas da kuma yankin tsakiyar Arewacin Najeriya.
Atiku Abubakar ne ya saba samun nasara a wadannan wurare, amma yanzu za a raba kuri’un ne tsakanin Atiku da Peter Obi."

- Tonye Princewill

Duk da ya fice daga APC mai mulki, an rahoto ‘dan siyasar yana cewa yana goyon bayan ‘dan takaran APC watau Tonye Cole ya zama gwamna a Ribas.

PDP BoT za su yi taro

Kuna da labari cewa a daren yau ne 'Yan majalisar BoT na jam’iyyar PDP suka yi zama da ‘Dan takaran Shugaban kasa, Atiku Abubakar a gidansa.

Da alama Adolphus Wabara zai jagoranci zaman farko na majalisarsa da nufin a dinke barakar da ta addabi jam’iyyar ta PDP kafin kamfe ya yi nisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng