Jagoran APC Ya Bayyana Kishin Bola Tinubu da Makusudin Barinsa Najeriya zuwa Ingila

Jagoran APC Ya Bayyana Kishin Bola Tinubu da Makusudin Barinsa Najeriya zuwa Ingila

  • Jigon APC, Hon Yakubu Murtala Ajaka, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Asiwaju Tinubu a matsayin mutum mai kishin kasa
  • Ajaka wanda ya kasance sakataren labaran jam'iyyar mai mulki yace Tinubu na Ingila cikin koshin lafiya kuma ba jinya ya je yi ba kamar yadda ake ta rade-radi
  • Ya kuma ce babban makasudin zuwan tsohon gwamnan na jihar Lagas Landan shine don ya tattauna da kungiyoyi daban-daban

Landan - Mataimakin sakataren labaran jam’iyyar All Progressives Congress, Hon Yakubu Murtala Ajaka, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na nan cikin koshin lafiya.

Hon. Ajaka ya kuma bayyana cewa sabanin yadda ake ta yayatawa, babban jigon na jam’iyya mai mulki ba jinya ya tafi yi a Ingila ba, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bidiyon dan takarar shugaban kasan PDP na tikar rawa ya jawo cece-kuce a kafar Twitter

Ajaka wanda ya ziyarci dan takarar na APC a Landan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki a yammacin ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.

Tinubu
Jagoran APC Ya Bayyana Kishin Bola Tinubu da Makusudin Barinsa Najeriya zuwa Ingila Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sabanin jita-jitan da abokan hamayyarmu a siyasa ke yayatawa cewa Sanata Bola Ahmed Tinubu ya tafi jinya a Landan. Duk karya ce.”

Jigon jam’iyyar ya bayyana cewa Tinubu ya tafi kasar ne don ganawa da kungiyoyi daban daban kan ci gaban kasar, yana mai cewa yana cikin koshin lafiya.

Ya kara da cewar Tinubu mutum ne mai tarin kwarewa a harkar siyasa da shugabanci, wanda ya fahimci yanayin Najeriya kuma zai yi amfani da wannan tarin sani wajen shugabanci idan har ya dare kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Ya kuma ce daga cikin ayyukan da dan takarar shugaban kasar zai yi harda hada kan kasar da damawa da matasa wajen jan ragamar manufofin kasar.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa ya fadi abu daya zai yi ya magance yajin ASUU

Hon. Ajaka ya kara da cewar cikin masu fafutukar neman kujerar shugabancin kasar a 2023, dan takarar APC shine na daban wanda ya kafa tarihi mai kyau.

Wasu Sunce Na Mutu, Sunce Na Janye, Amma Kwalelenku Ina Nan Lafiya: Tinubu

A gefe guda, mun ji cewa dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi watsi da jita-jitan da ake cewa jinya ya tafi birnin Landan.

Tinubu ya saki sabon bidiyon da dan tsokaci a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba, 2022.

Bidiyon mai tsayin sakwanni bakwai kacal ya nuna Tnubu yana motsa jiki kan keken tafi da gidanka cikin dakinsa a Landan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel