2023: Ina Tattauna Wa da Mambobin Jam'iyya da Suka Fusata, Atiku Ya Magantu
- Mai neman zama shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace har yanzu yana kokarin rarrashin mambobin PDP da suka fusata
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace sun fahimci cewa sun tafka kuskure amma suna kokarin gyara wa
- Atiku ya ziyarci jihar Gombe domin buɗe sabon Ofishin Kamfe amma wasu kusoshin PDP a jihar ba su halarci taron ba
Gombe - Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace bai hakura ba har yanzu yana tattauna wa da mambobin da suka fusata domin shawo kan rikicin da ya addabi jam'iyyar.
Daily Trust ta tattaro cewa Atiku ya yi wannan furucin ne ne a jihar Gombe, jim kaɗan bayan buɗe sabon Ofishin da jigon PDP, Jamilu Isiyaku Gwamna, ya ba shi.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya nuna alamun kwarin guiwa da cewa rikicin da ya ƙi ci kuma ya ki cinye wa za'a warware shi kuma PDP zata tunkari zaɓen 2023 da ƙarfinta.
Alhaji Atiku ya ƙara da cewa har yanzun PDP shahararriyar jam'iyya ce kuma mafi daɗe wa a Najeriya, haka nan ita ke da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun gano cewa mun tafka kuskure kuma muna aiki ba dare ba rana domin gyara wannan kuskure, sannan muna da yaƙinin 'yan Najeriya sun yi amanna da mu."
"Yan Najeriya zasu iya kwatanta ƙoƙarin mu da na abokan hamayya kuma ina da tabbacin banbanci a bayyane yake, haka zalika abinda muka yi kaɗai ya isa ya wakilce mu."
- Atiku Abubakar.
Jiga-jigan PDP sun kaurace wa taron
Jamilu Gwamna ya ba da kyautar Ofishin yaƙin neman zaɓe da ke kallon kallo da Ofishin mataimakin gwamna domin yin amfani da shi a matsayin Hedkwatar Atiku da sauran 'yan takarar PDP a zaɓe mai zuwa.
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Gombe, Jamilu gwamna ya sha kaye ne a hannun Muhammad Jibril Barde, ɗan takarar gwamna da PDP ta tsayar a zaɓen 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Legit.ng Hausa ta gano cewa mai neman zama gwamnan, shugaban PDP na jihar, Audu Kwaskebe, da wasu mambobin majalisar zartarwa ba su halarci taron buɗe Ofishin ba.
A wani labarin kuma Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Jita-Jitar Wani Gwamnan PDP Ya Jingine Atiku, Ya Goyi Bayan Obi a 2023
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙaryata labarin da ake yaɗa wa cewa ya bar Atiku, ya koma bayan Peter Obi a zaɓen 2023
Hadimin gwamnan, Crusoe Osagie, a wata sanarwa da ya fitar yace wasu masu son juya tunanin mutanen ne suka kirkiri labarin.
Asali: Legit.ng