Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Kishin-Kishin Gwamnan Edo Ya Mara Wa Peter Obi Baya a 2023

Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Kishin-Kishin Gwamnan Edo Ya Mara Wa Peter Obi Baya a 2023

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙaryata labarin da ake yaɗa wa cewa ya bar Atiku, ya koma bayan Peter Obi a zaɓen 2023
  • Hadimin gwamnan, Crusoe Osagie, a wata sanarwa da ya fitar yace wasu masu son juya tunanin mutanen ne suka kirkiri labarin
  • Ya tabbatar da cewa jagoran PDP a jihar Edo na nan a sahun gaba wajen yaƙin neman zaɓen jam'iyyarsa

Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗa wa cewa ya ayyana goyon baya ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi.

Gwamnan yace labarin ya koma bayan Obi ƙarya ce da ƙeta da wasu suka ƙirƙira saboda son ransu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki.
Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Kishin-Kishin Gwamnan Edo Ya Mara Wa Peter Obi Baya a 2023 Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Jaridar Punch tace ya faɗi haka ne a wata sanarwa da mashawarcin gwamnan na musamman kan harkokin kafafen watsa labarai, Crusoe Osagie, ya fitar.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Gwamnoni, Jiga-Jigan PDP da Basu Halarta Ba da Waɗanda Suka Halarci Taron Buɗe Kamfen Atiku

A sanarwan, gwamna Obaseki yace wasu masu neman ɓata masa suna ne suka ƙirkiri jita-jitar da nufin kawar da hankalin al'umma don cimma wata buƙatarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwan tace:

"Labarin da wasu kafafen watsa labarai suka buga da ke cewa gwamnan Edo, Godwin Obaseki, ya goyi bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, ba gaskiya bane.
"Babu wata sanarwa da ta nuna haka mai alaƙa da mai girma gwamna. Wasu dake kokarin ɓata masa suna ne suka kirkiri labarin domin kawar da hankalin al'umma da bayanan ƙarya saboda son rai."

Obaseiki na tare da Atiku - Osagie

Hadimin gwamnan ya ƙara da cewa, "Gwamna Obaseki na ɗaya daga cikin na sahun gaba a yaƙin neman zaɓen PDP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da abokin takararsa, gwamna Okowa.

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Wani Jigon Siyasa a Kano, Ya Koma Bayan Tinubu

"Obaseki ne jagoran jam'iyyar PDP a jihar Edo, kuma zai amfani da dukkan kwarewarsa wajen tabbatar da nasarar jam'iyyar da yan takarata a babban zaɓen 2023."

A wani labarin kuma Atiku Ya Nada Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Muhimman Mukamai

Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya sake yin wasu muhimman naɗe-naɗe a tawagarsa.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da Sanata Ibrahim Shekarau sun samu shiga sabon naɗin Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel