PDP Ta Tabbatar da Tura wa Mambobin NWC Miliyoyin Kudi, Amma Ta Ce Ba Cin Hanci Bane
- Dambarwar da ke ci gaba da faruwa a jam'iyyar PDP na sake daukar sabon salo, lamura sai kara rikicewa suke
- An samu rahoton da ke cewa, jam'iyyar PDP ta tura wa wasu jiga-jiganta kuma mambobin kwamitin ayyuka na NWC kudi don siye bakinsu
- Sai dai, jam'iyyar ta PDP ta fito ta yi bayanin kudaden da ta tura, kuma don me ta ba da su ga wadannan jiga-jigai
FCT, Abuja - Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta amince da cewa ta tura wasu miliyoyi zuwa asusun bankunan mambobin kwamitinta na ayyuka (NWC), amma ta musanta ba da kudin a matsayin cin hanci.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, martanin na PDP na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.
Rahoton ya ce, sanarwar da PDP ta fitar martani ne ga kalaman wasu mambobi da ke cewa sun mayar da N20m da aka basu tare da alanta cin hanci aka basu don zama kan wata magana.
Yadda rikicin ya faro
Rahotanni a baya sun ce, wasu mambobin NWC hudu sun karbi wadannan kudade, amma daga baya suka bayan da rahotanni suka yayata jita-jitar PDP ta ba mambobin cin hanci ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sunayen mambobin da ke cikin wannan dambarwa sun haka da:
- Mataimakin shugaban jam'iyyar a matakin kasa (yankin Kudu maso Yamma), Olasoji Adagunodo
- Mataimakin shugaban jam'iyyar a matakin kasa (yankin Kudu maso Yamma) Taofeek Arapaja
- Mataimakin shugaban jam'iyyar a matakin kasa (yankin Kudu) Dan Orbih
- Shugabar matan jam'iyya ta kasa, Stella Affah-Attoe
Kudin da aka ce na cin hanci ne, alawus din muhalli aka basu - martanin PDP
A cewar sanarwar da ke martani ga wadannan mambobi, Ologunagba ya bayyana karara cewa, an ba mambobin NWC wadannan kudaden ne a matsayin alawus na muhalli da jam'iyya ta amince a basu bayan bin tsarin da ya dace.
Ologunagba yace
“Domin kawar da shakku, PDP ta bayyana balo-balo cewa, babu kudin da aka tura asusun wani mamba na NWC a matsayin cin hanci saboda cimma wata manufa.
"Alawus na muhalli aka basu kuma ya bi tsarin da ya dace wanda jam'iyyar ta gindaya - daidai da tsarin aiki da kuma biyan hakkin ma'aikata da manyan jiga-jigai na jam'iyyar."
Daga karshe dai ya bukaci jama'a da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa don kawo rabuwar kai a jam'iyyar.
Tonon Sililin Wike: Shugabannin PDP 4 Sun Mayar Kudi N122m Da Aka Basu
A wani labarin, akalla mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP hudu sun mayar da kudi N122.4 million baitul malin jam'iyyar.
A wasikun da suka aikewa jam'iyar, mambobin sun bayyana cewa an tura wadannan kudade asusun bankunansu ne ba tare da izini ko sanninsu ba, rahoton ChannelsTV.
An ce kudin na cikin sama da Bilyan 10 na kudin cinikin Fom daga wajen yan takara.
Asali: Legit.ng