Tonon Sililin Wike: Shugabannin PDP 4 Sun Mayar Kudi N122m Da Aka Basu

Tonon Sililin Wike: Shugabannin PDP 4 Sun Mayar Kudi N122m Da Aka Basu

  • Rikicin jam'iyyar adawa ta PDP ya dau sabon salo yayinda shugabanni suka fara mayar da kudaden da aka tura musu
  • Gwamna Nyesom Wike a makon da ya gabata ya bayyana cewa shugaban PDP ya karbi cin hancin N1bn
  • Da alamun raba wadannan kudade akayi kuma an yanka ta tashi, Wike na shirin sake fasa wani kwan

Abuja - Akalla mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP hudu sun mayar da kudi N122.4 million baitul malin jam'iyyar.

A wasikun da suka aikewa jam'iyar, mambobin sun bayyana cewa an tura wadannan kudade asusun bankunansu ne ba tare da izini ko sanninsu ba, rahoton ChannelsTV.

An ce kudin na cikin sama da Bilyan 10 na kudin cinikin Fom daga wajen yan takara.

Mambobin kwamitin da suka mayar da kudaden sun hada da;

Kara karanta wannan

Rikici A Jam'iyyar APC: Abdullahi Adamu Ya Tuhumci Tinubu Da Yaudara

1. Mataimakin uwa jam'iyyar na Kudu, Taofeeq Arapaja

2. Mataimakin jam'iyya na yankin Kudu maso yamma, Olasoji Adagundo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

3. Mataimakin jam'iyya na yankin Kudu maso kudu, Dan Orbih

4. Shugabar Matan jam'iyyar, Prof. Stella Affah-Attoe.

Yayinda Adagunodo, Orbih da Effah-Attoe suka mayar N28.8 million da kowannesu ya samu, Arapaja ya mayar da N36m.

A wasikar da suka aikewa shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, sun bayyana cewa basu san dalilin biyansu wadannan kudade ba.

NWC Member
Tonon Sililin Wike: Shugabannin PDP 4 Sun Mayar Kudi N122m Da Aka Basu
Asali: Twitter

Effah-Attoe a wasikarsa tace:

"Da na ofishinka shin kudin menene, an fada min kudin hayan shekaru biyu ne. Amma tun da na karbi wadannan kudi aka rika kira na a waya cewa na karbi cin hanci don in goyi bayan shugaban uwar jam'iyyar sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsa da Gwamnan Rivers, Nyesom Wike."
"Saboda haka ina mai mayar da kudin asusun jam'iyyar."

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Wani Jigon Siyasa a Kano, Ya Koma Bayan Tinubu

Rikici Ya Barke a Kwamitin NWC Na Jam’iyyar PDP Akan Kudi Naira Biliyan 10 Na Fom Din Takara

Mun kawo muku cewa rikici ya sake barkewa a jam'iyyar kan yadda aka kashe kudin foma-foman da PDP ta siyar gabanin zabukan fidda gwani.

Kwamitin ayyukan PDP ne ke tado da wannan batu na sanin bahasin kashe Naira biliyan 10, inji rahoton The Nation.

Wasu mabobin NWC sun nuna damuwa game da yadda kudin ya zaftare daga Naira biliyan 10 zuwa Naira biliyan 1.

Batutuwan da ke fitowa sun ce, PDP na shirin ba dukkan mamban NWC da ke neman bahasi N28m domin rufe musu baki kan tado da sabon rikici a jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel