2023: Peter Obi Ya Bayyana Shirin Da Ya Yi Wa Yan Bindiga, Da Masu Neman Ɓallewa Daga Ƙasa Idan An Zaɓe Shi

2023: Peter Obi Ya Bayyana Shirin Da Ya Yi Wa Yan Bindiga, Da Masu Neman Ɓallewa Daga Ƙasa Idan An Zaɓe Shi

  • Mai fatan zaman shugaban kasa, Peter Obi ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da yan bindiga ba
  • Ya ce ba a bukatar yi wa kundin tsarin mulki kafin magance yan bindiga, amma ya ce akwai bukatar sake tsarin kasar
  • Peter Obi ya ce gwamnatinsa ba za ta ki sauraron masu neman ballewa daga Najeriya ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya sha alwashin ba zai yi sasanci da yan bindiga ba idan an zabe shi shugaban kasa a babban zaben 2023, The Cable ta rahoto.

Peter Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba yayin hira da aka yi da shi a Arise TV.

Peter Obi
2023: Peter Obi Ya Bayyana Shirin Da Ya Yi Wa Yan Bindiga, Da Masu Neman Ɓallewa Daga Ƙasa Idan An Zaɓe Shi. Hoto: Peter Obi.
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Zan saurari su Nnamdi Kanu, amma babu ruwana da 'yan bindiga, inji Peter Obi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da ya ke magana a hirar na talabijin, ya ce idan aka zabe shi gwamnatinsa za ta tattauna da masu neman ballewa daga kasa da wasu masu ruwa da tsaki.

Ya kara da cewa akwai bukatar a sake tsarin rabon albarkatun kasar amma ya ce hakan ba abu ne mai sauki ba kamar yadda wasu ke tunani.

A cewarsa:

"Akwai bukatar sauya tsarin rabon arzikin kasar, hakan alheri ne ga kasar. Za a yi sauyin ta kundin tsarin mulki amma zai dauki lokaci. Akwai abin da ya kamata ka magance. Ba sai ka jira irin wannan sauya tsarin kasar ba kafin ka fito da mutane daga talauci.
"Domin magance matsalar tsaro, ba ka bukatar sauya kundin tsarin mulki. Wadannan za su faru kuma hakan alheri ne ga kasa."

"Gwamnati na ba za ta zama na kama karya ba" - Peter Obi

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fara kamfen zaben 2023, jigon APC ya ce bai san inda Tinubu yake ba

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta yi mulkin kama karya ba kuma za ta warware matsaloli cikin zaman lafiya a kasar.

Ya ce:

"Zan tattauna da kowa saboda ka san cewa mun yi kokari kuma abin baya aiki."

A bangaren yan bindiga da wasu ayyukan batanci, ya yi gaggawan cewa ba zai tattauna da irin wannan mutanen ba.

Ya ce:

"Ba su cikin mutanen da zan tattauna da su. Yan bindiga yan bindiga ne, masu laifi masu laifi ne, wadanda hakan bai musu dadi ba, aiki na shine in dauki mataki kansu."

Peter Obi, ya kaddamar da kamfen dinsa a jihar Plateau a Jos, babban jihar.

Ka Ja Kunnen Magoya Bayan Ka, Tinubu Ya Gargadi Peter Obi Kan Yada Labaran Karya

A wani rahoto, Dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci takwararsa na Labour Party, Mr Peter Obi, ya ja kunnen magoya bayansa don su dena yada karya, makirci da aibanta shi da sauran yan takara.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Muke Ragargazan Yan Ta'adda Da Yan Bindiga, Gwamnatin Tarayyar Najeriya

Tinubu, cikin sanarwar da direktan watsa labaransa, Mr Bayo Onanuga ya fitar, ya bukaci Obi ya ja kunnen magoya bayansa kuma ya bari zaben 2023 ya zama kan batutuwan da za su bunkasa kasa, cigaba da kwanciyar hankalin Najeriya, yana gargadin "karya da yada maganganu marasa tushe za ba su saka a ci zabe ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164