Dalilin Da Yasa Muke Ragargazan Yan Ta'adda Da Yan Bindiga, Gwamnatin Tarayyar Najeriya

Dalilin Da Yasa Muke Ragargazan Yan Ta'adda Da Yan Bindiga, Gwamnatin Tarayyar Najeriya

  • Lai Mohammmed, Ministan Labarai da Al'adu ya ce gwamnatin tarayya na cigaba da ragargazan yan bindiga ne don samar da tsaro a kasar
  • Mohammed ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai a Calabar, babban birnin Jihar Cross Rivers
  • Ministan Labaran ya bawa yan Najeriya tabbacin cewa matsalar rashin tsaro na daf da zama tarihi musamman idan aka kwantanta 2015 da 2022

Cross Rivers - Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnati na cigaba da ragargazar yan ta'adda da masu tada kayan baya domin samar da tsaro a kasar.

Ministan ya bayyana hakan ne a Calabar yayin taron manema labarai tare da Gwamnan Cross River, Farfesa Ben Ayade, yayin bikin ranar yawon bude ido na duniya ta shekarar 2022.

Lai Mohammed
Dalilin Da Yasa Muke Ragargazan Yan Ta'adda Da Yan Bindiga, In Ji Gwamnatin Tarayyar Najeriya. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Gwamnoni 4 na Najeriya da Nijar Sun yi Muhimmiyar Ganawa a Maradi

Ya ce ana bukatar ayyukan gine-gine da tsaro kafin yawon bude idanu ya bunkasa, Vanguard ta rahoto.

Alhaji Mohammed ya ce:

"Zan iya bugun kirji a nan in ce cikin watanni uku da suka gabata, har masu sukar mu za su yarda cewa gwamnati ta fara samun nasara wurin samar da tsaro. A bangaren rashin tsaro, ina son tabbatar muku cewa abu mafi muni ya wuce."

Ya ce idan aka kwatanta halin da kasar ke ciki a shekarar 2015 da yanzu a 2022, babu shakka akwai hujoji da ke goyon bayan matsayin gwamnati na cewa ana samun cigaba.

Ministan ya ce:

"Abin takaici ne ganin mutanen da ke tsokaci kan rashin tsaro ba su duba halin da muke a 2015 da halin da muke a yanzu.
"A 2015, dukkan yankin arewa maso gabas ba wurin zuwa bane. Da aka nada ni Minista a 2015, daya cikin ayyukan da na fara shine zuwa arewa maso gabas, musamman Maiduguri, Kaure, Konduga da Bama tare da tawagar yan jarida na gida da kasar waje don ganin barnar da yan Boko Haram suka yi.

Kara karanta wannan

An kama fasto a jihar Arewa bisa bude asibiti a cocinsa, yana ba da maganin bindiga

"A ranar 5 ga watan Disamban 2015 muka tafi kuma sai da jiragen sojojin sama suka mana rakiya daga Maiduguri zuwa Bama, nisar kilomita 68 tsakaninsu. Baya ga ayyarin motoccin mu, ba mu ga wasu motocci ba. Boko Haram sun lalata dukkan gidajen da ke Bama. Babu makarantu da asibitoci a arewa maso gabas. An lalata layyukan sadarwa."

Zulum: Muna Sane Da Hatsarin Da Ke Tattare Da Shirin 'Sauya Tunanin Tubabbun Ƴan Ta'adda'

A wani rahoto, Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno yayin da yake amsar tubabbun ‘yan ta’adda ya ce gwamnati ba za ta makance wa hadarorin da ke tattare da shirin sabunta dabi’un tsofaffin ‘yan ta’addan ba, The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, akwai bukatar tsananta tsaro da kuma bin hanyoyi da dama wadanda zasu cire hadarorin da ke tare da shirin, kuma su tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel