Kotun Koli Ta Tabbatar da Ademola Adeleke a Matsayin Sahihin Dan Takarar Gwamnan Osun Na PDP

Kotun Koli Ta Tabbatar da Ademola Adeleke a Matsayin Sahihin Dan Takarar Gwamnan Osun Na PDP

  • Kotun koli ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin sahihin dan takarar gwamnan PDP a zaben fidda gwani
  • An kai ruwa rana a PDP a jihar Osun tun bayan da aka samu rabuwar kai a zaben fidda gwanin da aka yi a jihar
  • A yau dai kotun koli ta kawo karshen cece-kuce da ganin ni ke da gaskiya tsakanin 'yan takarar da suka fito

Jihar Osun - Kotun koli a ranar Alhamis 29 ga watan Satumba ta tattara da zababben gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke a matsayin sahihin dan takarar da ya lashe zaben gwamnan jihar a zaben ranar 16 ga watan Yulin bana, Vanguard ta ruwaito.

Babbar kotun ta yi zama tare da alkalai biyar, inda ta kori karar da Prince Dotun Babayemi ya daukaka don kalubalantar Adeleke a matsayin sahihin dan takarar gwamnan PDP.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Lawan Ya Bayyana Matsayinsa Kan Hukuncin Kotu Na Ba Wa Machina Takarar Yobe Ta Arewa

Ademola Adeleke ya tabbata sahihin dan takarar gwamnanPDP
Kotun Koli Ta Tabbatar da Ademola Adeleke a Matsayin Sahihin Dan Takarar Gwamnan Osun Na PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, an yi zabe a bangarori biyu na jam'iyyar PDP a jihar Osun gabanin zaben da aka yi a watan Yuli.

Lauyan mai shigar da kara, Mr Adebayo Adelodun (SAN), ya janye karar ne bayan da kwamitin alkalai karkashin jagorancin Amina Augie, ya ja hankalinsa kan cewa shari'ar ba ta da makama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamitin ya tabbatar masa da cewa karar ba ta da wani sahihanci, inda ta jaddada cewa an shigar da karar kwanaki 14 bayan ka'idar da doka ta tanada, haka nan Daily Sun ta ruwaito.

An sha samun matsalolin rashin fahimtar juna a jam'iyyun siyasa a Najeriya, lamarin da ka iya zuwa har gaban kotu tare da neman alkalai su raba gardamar da ta kunno kai.

Dalilai Biyu Ne Suka Ja Ahmad Lawan Ya Rasa Tikitin Takarar Sanata a Yobe

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Dalilai biyu da suka ja shugaban majalisar dattawa ya rasa tikitin takarar badi

A wani labarin, rikicin ko wanene zai zama dan takarar sanatan da hukumar zabe ta INEC ta amince dashi a APC a mazabar Yobe ta Arewa ya kawo karshe, domin an zabi Bashir Machina a matsayin dan takara.

Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin Fadima Murtala Aminu ta yanke hukunci a yau Laraba 28 ga watan Satumbam inda ta umarci INEC ta amince da Machina a matsayin dan takarar sanatan APC daga Yobe ta Arewa.

Tikitin takarar dai an jima ana kai ruwa rana akansa tsakanin Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa da Bashir Bachina tun bayan kammala zaben fidda gwanin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.