Gwamna Ya Mayarwa Buhari Martani Bayan Ya Tsawatar Masa Kan Siyawa Jami'an Tsaron Jiharsa Makamai

Gwamna Ya Mayarwa Buhari Martani Bayan Ya Tsawatar Masa Kan Siyawa Jami'an Tsaron Jiharsa Makamai

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sanarwa gwamnatin tarayya cewa makaman da zai bai wa Amotekun ne don kariya ga jama'a
  • Ya sanar da cewa rantsuwa kowanne gwamna ya dauka na bai wa jama'ar jiharsa kariya, don haka ba zai ci amana ba
  • Ya jaddada cewa, dalilan da Garba Shehu ya fadi daga fadar shugaban kasa ba su cika gamsassu ba da zasu hana shi mika makaman ba

Ondo - Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu yayi wa gwamnatin tarayya martani cewa nufinsa na siyan makamai ga rundunar Amotekun shine don bai wa jama'ar Ondo kariya.

Akeredolu
Gwamna Ya Mayarwa Buhari Martani Bayan Ya Tsawatar Masa Kan Siyawa Jami'an Tsaron Jiharsa Makamai. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Akeredolu ya bayyana cewa dalilan da hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayar na ci gaba da kin amincewa da amfani da nagartattun makamai da jami’an tsaron jiharsa, ba su da ma'ana a yayin da ake fuskantar kalubalen tsaro a jiharsa

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Farfesoshi Da Manyan Lakcarori 21 Suka Rasu A Jami'ar Tarayyar Najeriya Saboda Yajin Aikin ASUU

The Nation ta rahoto, Gwamnan Ondo ya ce gwamnatin jihar Katsina ba ta musanta furucinsa na amfani da AK47 ba da 'yan bangansu ke yi ba a lokacin horo.

Akeredolu ya tsaya kan cewa dole ne jami’an tsaron Amotekun da ke da goyon bayan doka a kowane yanki na kasar nan su samu damar mallakar makamai kamar yadda masu laifi ke yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa, a kula da kiran da kungiyar ‘yan sandan jihar ta yi, kuma a yi amfani da sauyi a inda ya cancanta.

A cewarsa:

“Kowane Gwamna ya rantse kan cewa zai kare jiharsa da jama’a. Dole ne a bar jiharsa ta sanya jami'an tsaro a matsayin rundunonin daidaitawa don tunkarar miyagun 'yan ta'addan.
“Lokaci ya yi da za mu tunkari wadannan ‘yan ta'adda tare da dawo da kwarin gwiwar jama’a. Ba za mu iya yin abu ɗaya akai-akai ba kuma muna tsammanin sakamako daban-daban."

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Akeredolu: Babu Gudu Babu ja da Baya kan Shirin Ba Sojojin Amotekun Makamai

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya ce babu gudu babu ja da baya kan matakin da gwamnatinsa ta dauka na siyo makamai da alburusai tare da rarrabe su ga jami’an tsaron jihar, Amotekun.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Akeredolu ya bayyana cewa, makaman da jihar za ta tallafa, za a yi amfani da su ne wajen yakar wadanda ya kira ‘yan daba masu aikata laifukan cin zarafi da zaluncin bil’adama.

Ya ce dole ne a yi amfani da karfin ikon jihar wurin yaki da masu tada hankali da masu rike da makamai wadanda ba hukuma ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng