Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Farfesoshi Da Manyan Lakcarori 21 Suka Rasu A Jami'a Saboda Yajin Aikin ASUU

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Farfesoshi Da Manyan Lakcarori 21 Suka Rasu A Jami'a Saboda Yajin Aikin ASUU

  • Manyan lakcarori 21, cikinsu har da farfesoshi, sun rasu a jami'ar tarayya ta Calabar a jihar Rivers
  • Rahoton ya kara da cewa lamarin haka ya ke a wasu jami'o'in kasar
  • Sun rasu ne sakamakon rashin biyan su albashi da gwamnati ta yi, duba da cewa mafi yawansu na da fama da rashin lafiya

Calabar, Cross River - Farfesoshi da manyan malamai fiye da 21 ne suka rasa rayyukansu a jami'ar tarayya ta Calabar, Jihar Cross Rivers.

A cewar Vanguard, malaman makarantan sun rasu ne saboda yajin aiki mai tsawo da kungiyar malaman jami'o'i na ASUU ke yi.

Jami'ar Calabar
Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Farfesoshi Da Manyan Malaman Jami'a 21 Suka Rasu Saboda Yajin Aikin ASUU. Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

Jaridar ta kara da cewa yawan mutanen da ke rasuwa na karuwa a jami'o'i daban-daban a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rashin biyan albashi ke janyo mutuwar lakcarori a jami'o'in Najeriya

Rahoton ya kara da cewa mambobin ASUU da dama sun rasu saboda rashin kudade da za su biya bukatunsu, musamman rashin lafiya.

Ta kara da cewa wasu ma'aikatan jami'ar wadanda ba masu koyarwa bane sun rasu saboda gwamnati ta tsayar da albashinsu.

Wani kwakwaran majiya, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, a jami'ar tarayya, ya ce malamai 21 ne suka rasu a UNICAL.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"A Jami'ar Calabar kawai, mun rasa fiye da malamai 21. Mun rasa ma'aikata marasa koyarwa da dama.
"Lokacin da SSANU da NASU suka dakatar da yajin aikinsu, an rahoto cewa lakcarori 21 ne suka rasu kuma daga lokacin zuwa yanzu, wasu sun kara mutuwa.
"Dalilin wannan mummunan abin shine rashin kudi. Baya ga matashin da ya rasu a gidansa saboda fashewar tukunyar gas, mafi yawancin sauran sun rasu ne saboda rashin kudi da za su kula da lafiyarsu."

Legit.ng Hausa ta samu damar ji ta bakin wata dalibar aji 3 a UNICAL yar asalin jihar Anambra wacce ta nemi a boye sunanta.

A hirar da suka yi a wayar tarho ta nuna damuwar matuka kan rasuwar daya daga cikin malaminsu Farfesa Gabriel U. Ntamu, tana mai cewa sauran malaman ba ta musu sani na sosai ba.

A cewarta:

"Babban rashi ne gare mu daliban UNICAL da ma wasu jami'o'in Najeriya da ya kan tafi zuwa koyarwa ta wucin gadi.
Mutum mai basira da kwarewa wurin aiki ga kuma mu'amala mai kyau.
"Muna fatan gwamnati za ta duba halin da malaman mu da harkar karatu ya ke ta cika musu alkawurran da ta dauka musu su dawo aji."

Dalibar ta ce ta gaji da zaman gida bayan shafe watanni suna sa rai amma har yanzu ba su cire rai ba.

Yajin Aikin ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowa Ya Yi Digiri Ba, In Ji Gwamnan APC

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi ya ce ilimin Jami'a fa ba na kowa da kowa bane, rahoton The Punch.

Umahi ya jadada cewa ba adalci bane a yi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.

Asali: Legit.ng

Online view pixel