Atiku Ya Fi Kowane Ɗan Takara Cancanta Ya Zama Shugaban Kasa a 2023, Namadi Sambo

Atiku Ya Fi Kowane Ɗan Takara Cancanta Ya Zama Shugaban Kasa a 2023, Namadi Sambo

  • Namadi Sambo, tsohon mataimakin shugaban kasa yace Atiku Abubakar ne ya fi dacewa ya gaji shugaba Buhari a 2023
  • Sambo, wanda ya halarci taron gabatar da litattafan Atiku da tawagar kamfe, yace ɗan takarar na da kwarewar da ake buƙata
  • Sai dai ya shawarci jam'iyyar PDP ta haɗa kai sannan ta jawo kowa a jiki domin cimma nasara a zaɓe mai zuwa

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, ya bayyana Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban kasa a inuwar PDP, a matsayin wanda ya fi dacewa da Najeriya a 2023.

Premium Times tace Sambo ya faɗi haka ne a Abuja a wurin taron gabatar da Litattafai kan Atiku da kaddamar da tawagar yaƙim neman zaɓen PDP.

Namadi Sambo.
Atiku Ya Fi Kowane Ɗan Takara Cancanta Ya Zama Shugaban Kasa a 2023, Namadi Sambo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewarsa, ba ko shakka Atiku ne mutumin da zai iya baje matsalolin Najeriya a faifai kuma yake da kwarewar lalubo hanyar warware su baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Jita-Jitar Wani Gwamnan PDP Ya Jingine Atiku, Ya Goyi Bayan Obi a 2023

"Atiku Abubakar direba ne a siyasa, wanda ba wai tuƙa mota bane kaɗai ya kware a kai, ya san hanyoyin da za'a bi wajen ceto Najeriya," Inji Namadi Sambo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, Namadi Sambo, ya shawarci PDP da cewa yayin da aka ƙaɗa gangar fara kamfe, yana da kyau a jawo kowa ya ba da tashi gudummuwar a dunƙule.

Mista Sambo ya ƙara da cewa, "Ku haɗa kai wuri guda kana ku tabbatar da cewa daga ƙarshe an kai ga nasara."

Zaɓen Atiku ba kuskure bane - Tsohon Gwamnan Anambra

A nasa jawabin, Jim Nwobodo, tsohon gwamnan jihar Anambra a jamhuriya ta biyu, yace yana da yaƙinin cewa 'yan Najeriya zasu dangwala wa ɗan takarar PDP a zaɓe mai zuwa.

Mista Nwobodo, a ayyana Atiku da cikakken ɗan Najeriya mai kishi, wanda zaɓensa ba zai zama kuskure ko dana sani ba. A kalamansa Yace:

Kara karanta wannan

2023: Ba Zan Bar 'Ya'Yana Su Fita Zuwa Ƙasashen Waje Ba, Atiku Ya Ɗau Sabbin Alƙawurra

"Muna neman shugaban ƙasa cikakken ɗan Najeriya mai gaskiya kuma na yi amanna Atiku ya kai matsayin. Tare da Atiku zamu samu dunƙulalliyar Najeriya. Ƙasar nan za ta yi kyau a hannunsa.

A wani labarin kuma mun haɗa muku Jerin Sunayen Gwamnoni, Jiga-Jigan PDP da Basu Halarta Ba da Waɗanda Suka Halarci Taron Buɗe Kamfen Atiku

Gwamnoni biyar ciki har da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, da wasu ƙusoshin PDP ba su halarci taron buɗe kamfen ɗin Atiku ba.

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da wani tsohon ministan duk ba'a gansu a wurin taron ba wanda ya gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262