Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Gwamna PDP Na Jihar Ogun
- An samu tsaiko a jihar Ogun yayin da kotu ta soke zaben fidda gwanin gwamnan PDP da aka yi a jihar
- An umarci PDP ta zabi wani lokaci a nan gaba domin sake sabon zaben fidda gwani mai inganci a jihar
- A makon da ya gabata ne aka sake zaben fidda gwanin gwamnan jihar Zamfara biyo bayan rushe na farko da kotu ta yi
Jihar Ogun - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abeokua, babban birnin jihar Ogun ta soke zaben fidda gwanin gwamnan da jam'iyyar PDP ta gudanar a jihar.
A jihar Ogun, an samu tsaiko a PDP yayin da aka samu bangarori uku da suka gudanar da zaben fidda gwani daban-daban, The Nation ta ruwaito.
Daya daga ciki, ya samar da Hon. Ladi Adebutu a matsayin wacce ta lashe zaben, kuma ita za ta gwabza a babban zaben 2023.
Sai dai, mai sharia Oguntoyibo ya rushe zaben fidda gwanin, inda ya ba da umarnin sake sabon zaben a wani lokaci mai aminci a nan gaba cikin kwanaki 14, rahoton Tribune Online.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda aka shigar da karar neman soke zaben
Prince Adesun Seriki da wasu mutum uku ne ya shigar da karar kalubalantar zaben fidda gwanin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kuma jam'iyyar PDP a jihar suka gudanar.
Prince Serike da sauran mutanen uku sun nemi kotu ta ba su 'yancinsu na zama su ne 'yan takarar gwamna a jihar ta Ogun, lamrin da ya gaza samun mafita.
Daga nan ne kotu ta umarci a sake zaben domin tabbatar da ingancin wanda ya cancanci zama dan takarar PDP.
Jam’iyyar PDP a Zamfara Ta Fara Shirye-Shiryen Sake Zaben Fidda Gwanin Gwamna
A wani labarin, jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta fara gudanar sabon zaben fidda gwanin gwamna gabanin babban zaben 2023 mai zuwa badi, Channels Tv ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da babbar kotun tarayya ta rusa zaben fidda gwanin da aka gudanar a watannin baya, wanda ya samar da Dauda Lawan a matsayin dan takarar gwamna.
Hukuncin kotun ya samo asali ne daga karar Ibrahim Shehu da wasu 'yan takara biyu na jam'iyyar suka shigar, inda suka kalubalanci sakamakon zaben.
Asali: Legit.ng