Abubuwa 5 da Ke Faruwa Duk Lokacin da Aka Fara Kamfen a Najeriya

Abubuwa 5 da Ke Faruwa Duk Lokacin da Aka Fara Kamfen a Najeriya

  • Wayar da kan masu kada kuri'u, 'yan a mutun jam'iyya da sauran 'yan Najeriya na daga cikin abin da ya kamata ya zama kan gaba nan da zaben 2023
  • Hakazalika, sa'o'i kadan suka rage a buga gangar siyasa, kuma jam'iyyun siyasa sun shirya tsaf don fara gangami a zagayen kasar nan
  • A bangare guda, akwai abubuwan da 'yan Najeriya ya kamata su sani game da matsaloli da abubuwan da ke faruwa a filin kamfen

Najeriya - A kasa da sa'o'i 24 za a fara gangamin kamfen din zaben 2023, lokacin da 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa za su kada gangar siyasa don tallata 'yan takararsu.

Tuni jam'iyyun siyasa suka fara shirya yadda za su fara kamfen din, jam'iyyu sun kafa kwamitocin kafar gangami a sassa daban-daban na kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP

A baya can, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa, a ranar Laraba 28 ga watan Satumba ne za a fara kamfen din zaben 2023 a Najeriya.

Abubuwa 5 da ke faruwa a lokacin kamfen a Najeriya
Abubuwa 5 da Ke Faruwa Duk Lokacin da Aka Fara Kamfen a Najeriya | Hoto: cnn.com
Asali: UGC

Sai dai, akwai bukatar 'yan Najeriya su san abubuwan da ke tattare da buga gangar siyasa a Najeriya kasancewar wasu abubuwa da dama za su faru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A takaice, mun tattaro muku abubuwa 5 masu muhimmanci da za su faru a lokutan kamfen a Najeria.

1. Cunkoso

Musamman a jihohi irin Legas, akwai yiwuwar gari ya cabe da cunkoso kasancewar tarukan kamfen na tara yawan jama'a.

2. Turmutsutsu

Wannan na daya daga cikin illolin da kamfen ke kawowa. Mutane za su yi tururuwa, don haka akwai yiwuwar a iya tumurmusa wasu mutane a filayen kamfen.

Wani rahoton Daily Trust ya ce, an samu irin wannan zaben 2019 a filin wasannin Fatakwal ta jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

An naqalto cew,a taron mutanen da suka zo ganin 'yan takarar da suke so ya yi yawa, don haka aka yi ta tururuwa har ta kai mutane na tattake junansu.

Akalla mutane 15 ne suka a wannan ranan.

3. Sayen masu kada kuri'u

Na daya daga cikin matsalolin da kamfen ke zuwa dashi ake raba kudade ga wadanda za su kada kuri'u.

A irin wadannan taruka, 'yan siyasa na raba kudi ga jama'a domin su zabe su a zabuka masu zuwa.

4. Yankan aljihu

A tarukan addini ma akan yi yankan aljihu balle kuma taron siyasa. Daya daga cikin irin abubuwan da zasu faru shine yawaitar yiwa mutane sata.

Matukar baka kula ba, akwai yiwuwar ka rasa wayarka a cikin cunkoso, domin kuwa idan ka yi sake, wani ne zai yanke aljihunka ya fauce komai da ke ciki.

Shawari dai waya a ajiye ta agida, hakanan katunan ciran kudi, makullai, lalita da sauran abubuwan da ake sakawa a aljihu.

Kara karanta wannan

Sabon rikici a PDP yayin da aka nemi N10bn na foma-fomai, aka rasa inda suka shiga

5. Fada akan 'yan takara

Ba sabon abu bane a ga matasa na kashe junansu saboda 'yan takara. To, a lokutan kamfen, akan samu irin wadannan matsaloli na yawaitar fadace-fadace tsakanin 'yan siyasa.

Irin wadannan matsaloli sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, kuma akwai yiwuwar a wannan kamfen da aka fara, a samu irin wadannan, don haka ya kamata a kula.

Rikici Ya Barke a Kwamitin NWC Na Jam’iyyar PDP Akan Kudi Naira Biliyan 10 Na Fom Din Takara

A wani labarin, awanni 48 kafin fara gangamin kamfen na PDP, rikici ya sake barkewa a jam'iyyar kan yadda aka kashe kudin foma-foman da PDP ta siyar gabanin zabukan fidda gwani.

Kwamitin ayyukan PDP ne ke tado da wannan batu na sanin bahasin kashe Naira biliyan 10, inji rahoton The Nation.

Wasu mabobin NWC sun nuna damuwa game da yadda kudin ya zaftare daga Naira biliyan 10 zuwa Naira biliyan 1.

Kara karanta wannan

Jerin 'yan siyasan Najeriya su da ke da jirage akalla 2 mallakin kansu, ba na haya ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.