An Gargadi Tinubu Kan Shirinsa Na Amfani da Kudi Wajen Raba Kawunan Kiristoci a Zaben 2023
- Dattawan kirista a arewa sun yi gagarumin gargadi ga APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu gabannin zaben 2023
- Kungiyar Kiristocin ta nemi Tinubu da ya daina amfani da kudi wajen kawo rabuwar kai a tsakanin al'ummar kirista musamman a arewacin Najeriya
- Tikitin Musulmi da Musulmi na jam'iyyar APC na ci gaba da shan suka musamman daga kungiyoyin kirista
An gargadi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan amfani da kudi wajen kawo rabuwar kai tsakanin Kiristoci.
Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kungiyar dattawan Kirista a jihohin arewa, dauke da sa hannun shugabanta, Oyinehi Inalegwu, a ranar Talata, 27 ga watan Satumba, jaridar Punch ta rahoto.
Sanarwar ta ce:
Kwararan Majiyoyi Sun Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa APC Ta Dakatar Da Fara Kamfen Har Sai Baba Ta Gani
“Mun gargadi APC da ta daina amfani da kudi don dauka da haddasa rabuwar kai a tsakanin Kiristoci, musamman a arewa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kungiyar ta NOSCEF ta ce APC na haddasa rabuwar kai tsakanin Kiristoci ta hanyar yin hayar wasu kungiyoyin kirista da ba a sani ba don saba hukuncin da kungiyar kiristocin Najeriya ta dauka.
Tun farko dai kiristoci sun fito sun nuna adawarsu da tsayar da Kashin Shettima da APC tayi a matsayin abokin takarar Tinubu.
Kungiyar ta ci gaba da cewa a watan Disambar 2021, Tinubu ya gana da wata kungiyar a Abuja sannan ya siyarda tikitin Musulmi da Musulmin, rahoton TheEagle.
“Mun yi gargadin cewa duk wani dan takarar shugaban kasa mai kishin kasa ya guji tikitin addini guda don gujewa rabuwar kasar ta bangaren addini.
“Kafin fara zaben fidda gwanin, NOSCEF ta sake gargadin yan takarar shugaban kasa a kan tikitin addini guda a Najeriya tana mai rokon hadin kai, adalci da kuma gaskiya.
“Saboda akwai wata daddadiyar manufa da take son cimma, APC ta yi gaban kanta kan tikitin addini guda, da nufin bi ta kan siyasar addini don yin nasara."
Kungiyar ta nuna rashin yarda kan tafarkin da jam’iyya mai mulki ke bi, a kokarinta na ganin ta ja hankalin jama’a da kuma samun karbuwa ta hanyar sako kungiyoyin addinin kirista da ba a san da su ba don lamunce masu.
Legit.ng ta tuntubi wani marubuci mai suna Mallam Muhammad Auwal don jin ta bakinsa game da tasirin wannan garagadi da kungiyar kiristocin arewa ta yiwa Tinubu, inda yace abu ne mai wuya.
Ya ce:
"Da farko dai siyasa irin ta Najeriya da ake bugawa a yanzu sai da kuɗi, duk sahihancin ɗan takara idan ya rasa kuɗi jama'a ba zaɓarsa zasu yi ba. Fitar da kuɗi na gyara alaƙar ɗan takara da masu kaɗa ƙuri'a ba tare da la'akari da bambancin addini ba.Haka zalika ɗan takara na buƙatar kuɗi wajen tarban baƙinsa a siyasance tare da karramasu.
"Na tabbata babban ɗan takara kamar Tinubu zuwa ya samu ƙungiyoyi fiye da hamsin da suka kai masa ziyara, sakamakon ɗaruruwan ƙungiyoyi na nan suna gogoriyon ganawa da shi, kuma aƙalla sai ya basu kuɗin motar komawa inda suka fito.
"Toh wai ma mutum Kirista ko Musulmi idan zai amshi kuɗi daga ɗan takara sai ya faɗa ma Malaminsa ko Fastonsa ne, balle a wasan mabiya wani addine suka fi amsa ko kuwa?
"Gaskiya abinda ƙungiyar ta faɗi ra'ayi ne kawai tsantsa na ƙashin kanta wanda baya rasa nasaba da ƙinsa da suke yi a siyasance sakamakon ɗauko mataimaki Musulmi.
"Hakan damansu ne, amma tabbas basu da hurumin hana shi baiwa waɗanda ya ga dama kuɗi don su zaɓe shi, ko hana wasu mutane karɓar kuɗin da ya basu."
Dan Takarar Shugaban Kasa, Rabiu Kwankwaso Ya Ziyarci Gwamnan APC A Arewa, Sun Sa Labule
A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Kwankwaso, ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Kwankwaso ya ziyarci Masari wanda ya kasance gwamna karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a rahar Lahadi, 25 ga watan Satumba.
Kamar yadda ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na twitter, dan takarar shugaban kasar na NNPP ya ce sun tattauna batutuwan da suka shafi kasar a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng