Shekarau Ya Zama Ala-ka-kai a NNPP, INEC tace Dole Shi ne ‘Dan takaran Jam’iyya

Shekarau Ya Zama Ala-ka-kai a NNPP, INEC tace Dole Shi ne ‘Dan takaran Jam’iyya

  • Hukumar INEC ta ki cire sunan Ibrahim Shekarau a matsayin ‘dan takaran Sanatan tsakiyar jihar Kano
  • Wani jami’in INEC yace a iyaka saninsu, Shekarau zai yi jam’iyyar NNPP takara, ba su san ya koma PDP ba
  • Sabuwar dokar zabe tayi tsauri a kan janye takara, hakan ya sa NNPP take fuskantar barazana a 2023

Abuja - Hukumar gudanar da zabe a Najeriya tayi bayanin abin da ya sa ta gaza sauya ‘dan takaran jam’iyyar NNPP na kujerar Sanatan tsakiyar jihar Kano.

Premium Times ta rahoto hukumar INEC tana cewa ba zai yiwu a maye gurbin Malam Ibrahim Shekarau da wani ‘dan takara, duk da ya canza sheka ba.

Shugaban sashen shari’a na INEC na reshen jihar Kano, Suleiman Tahir ya shaidawa manema labarai cewa sabuwar dokar zabe ba ta bada damar canjin ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

Da yake bayani a makon nan, Malam Suleiman Tahir ya nuna INEC ba ta san da maganar janye takarar tsohon gwamnan ba, domin ba a sanar da ita ba.

Sabuwar dokar zabe ta zo da canji

Sabuwar dokar zabe ta shekarar 2022 ba ta bada dama a cire sunan ‘dan takara haka kurum ba, sai idan ya rubuto takardar janye takararsa ko kuma ya mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sabuwar dokar tace da zarar an sa sunanka da farko, kafin a fitar da sunayen karshe na ‘yan takara, mai takara zai rubutawa INEC, ya hada da hotonsa.
Ibrahim Shekarau
Shekarau kafin ya bar NNPP Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Facebook

Sai ya sanar da INEC (ko ta sanar) janyewa daga takarar, ko kuma idan mutum ya mutu.
A irin haka ne ake sauya ‘dan takara, mutum ya janye bayan an fitar da sunan shi. Shekarau bai yi ko daya daga cikin wadannan abubuwa biyu ba.”

Kara karanta wannan

"Ba Kuskure Bane" Jam'iyyar APC Ta Faɗi Dalilin Sanya Jigon PDP a Kamfen Tinubu, Ta Maida Martani Ga Gwamnoni

- Suleiman Tahir

PDP: Ba mu san an yi ba - INEC

A matsayinta na hukuma da ke aiki da doka da tsari, jami’in na INEC yace a hukumance, ba su da masaniyar Sanata Shekarau ya bar jam’iyyar NNPP.

Babu wata takarda da Sanatan na Kano ta tsakiya ya rubutawa hukumar zabe mai zaman kanta domin tabbatar da cewa ya fasa yin takara a zaben 2023.

NNPP ta na fuskantar cikas a zabe

The Nation tace shugabannin NNPP ya rubutawa INEC takarda a kan batun.

Legit.ng Hausa ta fahimci matakin da INEC ta dauka zai shafi jam’iyyar NNPP a zaben Sanatan kudancin Taraba da tsakiyar Kano da wasu kujeru a Yobe.

Hanga zai koma Majalisa?

Kwanaki kun samu rahoto da ya nuna Sanata Rufai Hanga ya samu damar komawa majalisar dattawa domin wakiltar tsakiyar Kano a zabe mai zuwa.

An ji jam’iyyar NNPP ta tabbatar da Rufai Hanga a matsayin ‘dan takaran Sanatan Kano ta tsakiya Hanga da nufin ya maye gurbin Ibrahim Shekarau.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Peter Obi Na Kara Yin Suna Da Karfi, Babban Jigon APC Ya Yi Hasashe Mai Karfi

Asali: Legit.ng

Online view pixel