2023: Jerin ‘Yan shekara 20 Zuwa 30 da suka Shiga Takarar Majalisar Tarayya
A wannan rahoto, Legit ta tattaro yadda matasa suka fito neman takarar kujerun siyasa a zaben 2023.
Daga cikin fitattun masu neman takarar majalisar wakilan tarayya akwai Oluwajomiloju Fayose John, Abdussamad Dasuki da Bello El-Rufai.
‘Yan takaran Majalisar Dattawa
A ‘yan shekara 30 masu neman zama Sanatoci a zabe mai zuwa, mafi karancin shekarun da Legit.ng Hausa ta samu shi ne ‘yan shekara 35 a Duniya.
Ga jerin matasan da suka samu tikitin majalisar dattawa a jam’iyyun siyasa, da za su za a gwabza a mazabu dabam-dabam da ake da su a kasar nan a 2023.
1. Ahijo Karlahi Ibrahim
2. Abdulhafiz Saidu
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
3. Muhammed Sheriff
4. Ukpong Chuwang Daniel
5. Orok Gloria Odidi
6. Akhimie Kingson
7. Salisu Shamwilu
8. Bala Chichet
9. Yohanna Abimiku
10. Idris Musa Aliyu Nasarawa
11. Fyenda Timlok
12. Muhamma Usman
13. Umar Musa
14. Nubuya Pilinga
15. Musa Ibrahim Idris
16. Isa Buhari
17. Olasupo Ibraheem Olanrewaju
18. Adekunle Elizabeth Oyewumi
19. Urudeen Ojedokun Temileyi
20. Muhammed Gummi
21. Andrew Paul
22. Mumolen Irene Christopher
23. Saidu Ahmed
24. Ulu Joseph
25. Hammadu Ahmadu
Majalisar Wakilan Tarayya
A jihohi irinsu Benuwai, NNPP da ADP sun tsaida matasa suyi takarar majalisar wakilan tarayya.
Legit.ng Hausa ta fahimci a Cross River, Delta, da Ebonyi, akwai masu shekara 30 zuwa 40 da ke takara. A Sokoto, ADC ta tsaida Habiba Gidado mai shekara 29.
Haka zalika a jihar Neja, LP. NRM da APP sun tsaida matasa. Akwai ‘yan kasa da shekara 40 akalla hudu da ke takara a Katsina, haka abin yake a Enugu da Edo.
Chiroma Adamu Abidu
Bilyaminu Zaharadeen
Ali Muhammad
Suraja Ahmad Kiyawa
Shuaibu Mudansir Maigatari
Umar Usaini
Rufai Lawal
Alhassan Abdussamadan
Ayuba Jibril
Joseph Justine Zugwai
Zakari Muhammad Ahmad
Muhammad Murtala
Ibrahim Salisu
Abdulhamid Abdulrasheed
Sa’adatu Usman
Siraju Abullahi
Abubakar Yau
Rayyanu Muhammad Kolo
Abubakar Bawuro Rilwan
Habiba Gidado
Tersur Joseph
Muhammad Mustapha Abio
Ali Ahmed Usman
A Kano akwai matasa kusan 30 da ke takarar majalisa a 2023. Mun tattauna da Muktar Mudi Sipikin wanda ya fito takara a mazabar Fagge a karkashin PRP.
A jerin na mu, ba mu kawo sunayen 'yan takaran da suka fito daga jihar Kano ba.
Za mu kai labari - Matasa
Shi ma Yusuf Abdullahi Ahmad wanda aka fi sani da Yusuf Da'awah, ya yi magana a Facebook, yace yana sa ran doke 'dan shekara 62 da mai shekara 59 a Duniya.
Zaben 2023: Jerin Sunayen Jaruman Fina-Finan Najeriya 24 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu
Mukhtar Mudi Sipikin yace babu shakka matasa suna fuskantar matsalar kudi, amma suna wayar da kan al’umma su zabi jam’iyyu masu akida a 2023.
Matashin mai shekara 31 yace idan ya zama ‘dan majalisa, zai yi sanadiyyar bude cibiyoyin koyon sana’o’in zamani wanda za su amfana da matasa 8000.
Tarihin NGF a Najeriya
Kun samu labari a shekarar 1999 aka kafa kungiyar, amma babu wanda ya karfafa NGF kamar Dr. Bukola Saraki a lokacin yana Gwamna a jihar Kwara.
Kafin Aminu Tambuwal, gwamnoni irinsu; Rotimi Amaechi, Abdulaziz Yari, da Kayode Fayemi sun rike kujerar shugaban kungiyar NGF a kasar nan.
Asali: Legit.ng