Zaben 2023: Jerin Sunayen Jaruman Fina-Finan Najeriya 24 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu

Zaben 2023: Jerin Sunayen Jaruman Fina-Finan Najeriya 24 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu

Jam'iyyar All Progressive Congress, APC, a nada wasu fitattun jaruman masana'antar fina-finan kudancin Najeriya, Nollywood, a matsayin mambobin kwamtin kamfen din shugaban kasa na Bola Tinubu.

Ana sa ran za su taka muhimmin rawa wurin ganin dan takarar na APC ya samu nasara a babban zaben na 2023 da ke tafe.

Jaruman Nollywood
Zaben 2023: Cikakken Jerin Sunayen Jaruman Fina-Finan Najeriya Da Ke Cikin Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu. Hoto: (Photo: @tsg2023, @jideprince, @RealZackOrji)
Asali: Twitter

Daya daga cikin manyan mutanen daga masana'antar shine Zack Orji wanda aka a matsayin dareka na masu wasan kwaikwayo (PFA). Ana fatan Orji zai yi aiki a yankin kudu maso gabas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata taurariyar Nollywood da ta samu shiga jerin ita ce Foluke Daramola wacce aka nada a matsayin hadimar gwamnan Jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Budewa Motocin Tawagar Kamfen Sanata Uba Sani Wuta A Kaduna, An Sace Jiga-Jigan APC

Kazalika, Jide Kosoko, fitaccen kwararren jarumi, wanda aka nada matsayin sakatare a Legas.

Saura sun hada da Saheed Balogun, Gentle Jack, Benedict Johnson, Bimbo Akintola, Fathia Williams, da wasu da dama a masana'antar.

Baki daya, su guda 24 da suka samu shiga kungiyar kamfen din na Tinubu mambobi ne na kungiyar masu wasan kwaikwayo.

Ga cikakken jerin a kasa:

Jerin sunaye
Yan Nollywood 24 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Takarar Tinubu.
Asali: Twitter

2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

A wani rahoton, mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.

Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Kara karanta wannan

2023: Cikakkun Sunayen Yan Kannywood Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu

Yan takarar hudu sun ce sun janye goyon bayansu ga Kwankwaso suka koma goyon bayan Tinubu saboda rufa-rufa da ake yi wurin gudanar da harkokin jam'iyyar a matakin kasa, The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel