Kakakin Kamfen Ɗin Atiku Ya Fallasa Dalilin Da Yasa Osinbajo Da SGF Suka Ƙi Shiga Kwamitin Kamfen Ɗin Tinubu

Kakakin Kamfen Ɗin Atiku Ya Fallasa Dalilin Da Yasa Osinbajo Da SGF Suka Ƙi Shiga Kwamitin Kamfen Ɗin Tinubu

  • Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Daniel Bwala, ya yi ikirarin cewa Osinbajo da Boss Mustapha sun ce a cire daga kwamitin kamfen din APC
  • Bwala, ya ce rashin goyon bayan tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar na APC ta yi ne yasa suka janye daga kwamitin yakin neman zaben
  • Festus Keyamo, mai magana da yawun kamfen din Tinubu/Shettima ya yi martani yana mai cewa ba a saka Osinbajo da Mustapha bane don su mayar da hankali kan aiki

Twitter - Daniel Bwala, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya ce ya jinjinawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, SGF, saboda 'kin amincewa' da tikitin musulmi da musulmi na jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023

Bwala ya yi wannan martanin ne kan rashin saka sunan Osinbajo da Mustapha daga jerin sunayen wadanda ke kwamitin kamfen din shugaban jam'iyyar APC na shugaban kasa.

Mr Bwala
Tikitin Musulmi Da Musulmi Ya Hana Osinbajo Shiga Kwamitin Kamfen Din APC. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tunda farko, Legit.ng ta rahoto cewa babu sunan su cikin jerin sunayen mambobin kwamitin kamfen din na jam'iyyar APC.

Rashin yarda da tikitin musulmi da musulmi yasa babu sunan Osinbajo da Mustapha a kamfen din Tibubu - Bwala

Da ya ke martani ta shafinsa na Twitter a ranar Asabar, Bwala ya yi ikirarin cewa mutane biyun ne suka ce kada a saka sunansu.

Ya rubuta:

"Mun jinjinawa jarumtar Farfesa Osinbajo da Boss Mustapha saboda kin amincewa da tikitin MM ta hanyar cewa kada a saka su a kwamitin kamfen din APC. Ka da ku yarda da siyasar addini. Yan Najeriya za su raba gardama a yayin zabe."

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

Martanin Keyamo Ga Bwala

Bayan rubutun da Bwala ya yi a Twitter, Festus Keyamo, kakakin yakin neman zaben Tinubu, ya fitar da sanarwa don kara haske kan lamarin.

Keyamo ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bukaci kada a saka sunan mataimakin shugaban kasar don 'bashi damar ya mayar da hankali kan mulkin kasa da gwamnati.

Ya ce:

"An janyo hankalin mu kan wasu labarai da ke yawo cewa akwai yiwuwar matsala a gidan jam'iyyar APC saboda sunan mataimakin shugaban kasar mu da muke girmamawa, Farfesa Yemi Osinbajo, SAN, GCON, ba ya cikin kwamitin kamfen din Tinubu/Shettima.
"A matsayin mu na jam'iyya da gwamnati na gari, ba zai yiwu dukkan manyan jami'an gwamnati su yi watsi da matsayinsu saboda kamfen ba. APC na da hakkin yi wa yan Najeriya aiki har zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023, kuma muna da niyyar yin hakan."

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Bamu Sa Sunan VP Yemi Osinbajo A Kwamitin Kamfen Ba, Jam'iyyar APC

Zaben 2023: Jerin Sunayen Jaruman Fina-Finan Najeriya 24 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu

A wani rahoton, jam'iyyar APC ta nada wasu fitattun jaruman masana'antar fina-finan kudancin Najeriya, Nollywood, a matsayin mambobin kwamtin kamfen din shugaban kasa na Bola Tinubu.

Ana sa ran za su taka muhimmin rawa wurin ganin dan takarar na APC ya samu nasara a babban zaben na 2023 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164