2023: Atiku Ya Kara Shiga Tsaka Mai Wuya, Wasu 'Ya'yan PDP a Arewa Sun Koma Tsagin Wike
- Wasu matasan jam'iyyar PDP a arewa sun koma bayan tsagin Gwamna Nyesom Wike, inda suka nemi lallai sai Ayu ya yi murabus daga kujerar shugabancin jam'iyyar
- Matasan wadanda suka gudanar da zanga-zanga a a Kaduna sun bayyana cewa PDP ba jam'iyyar arewa bace
- Sun ce sai a nuna adalci da daidaito sannan za su yi nasara harma su lashe zaben shugaban kasa a 2023
Kaduna - Wata gamayyar kungiyar matasan jam’iyyar adawa a arewa, ta bukaci shugaban jam’iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus.
Kungiyar a wata zanga-zanga da ta gudanar a sakatariyar PDP da ke Kaduna a ranar Juma’a, ta ce ya zama dole shugaban jam’iyyar na kasa ya cika alkawarinsa sannan yayi murabus, jaridar Punch ta rahoto.
Jam’iyyar dai ta fada rikici tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya lashe tikitin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Kakakin kungiyar, Mista Shehu Isa-Dan’Inna, ya bayyana cewa PDP ba jam’iyyar arewa bace, amma jam’iyyar kowa ce, imma daga arewa ko kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Jam’iyyar Peoples Democratic Party ba jam’iyyar arewa ko kudancin kasar bane, ya zama dole mu zamo masu adalci da hadin kai, don mu samu damar lashe zabe a dukkan matakai a babban zaben 2023. Idan rikicin cikin gida yaki cinyewa, bana tunanin zamu lashe zaben shugaban kasa.
“Domin PDP ta nuna adalci kamar yadda take yi a kodayaushe, bai kamata arewa ta rike kimanin manyan mukamai uku a jam’iyyar ba.”
Isa-Dan’Inna, wanda ya bayyana cewa wasu gwamnonin PDP da shugabanni musamman daga kudancin Najeriya sun nace kan haka ne don adalci, ya ca bai kamata arewa ta rike tikitin shugaban kasa na jam’iyyar da kuma mukamin shugaban jam’iyya na kasa ba.
Ya ce kasar Najeriya na bukatar PDP a saman harkokinta domin dukka lamuran da suka shafi rayuwar yan Najeriya.
Ya ci gaba da cewa:
“Kimanin gwamnoni shida na yaki da gwamna daya. A kudu muna da kimanin yan takarar shugaban kasa hudu da suka fito daga jam’iyyu daban-daban wanda ya rage yawan kuri’unmu, kuma jam’iyyar mai mulki ma tana da karfi a kudu.
“Wike ma na da karfi, bama so mu raba kuri’unmu, wannan ne dalilin da yasa muke kira ga Iyorchia Ayu da ya yi murabus.
“Zai fi dacewa a garemu mu rasa Ayu a matsayin shugaban PDP da kuma lashe kujerar shugaban kasa, fiye da ace mun barsa sannan mun rasa kujerar shugaban kasa.”
Ya kuma bukaci kwamitin amintattu na PDP da kwamitin NWC da su yi adalci don nsarar jam’iyyar, rahoton Vanguard.
Rikcin Jam'iyyar PDP Na Nuna Wa 'Yan Najeriya Akwai Hadari a 2023, Wike
A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP ka iya shafar damar da take da shi na samun nasara a babban zaɓen 2023.
Daily Trust ta ruwaito gwamna Wike na cewa a halin yanzu PDP na faɗa wa 'yan Najeriya kar su kuskura su ba ta amana idan aka yi la'akari da yadda jam'iyyar ta gaza shawo kan rikicinta.
Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin hira da manema labarai a gidan gwamnatinsa dake Patakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Jumu'a.
Asali: Legit.ng