Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014

Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana yadda Atiku Abubakar, Bukola Saraki Tambbuwal da sauransu suka ki sauraron Jonathan a 2014
  • Ya bayyana yadda Jonathan ya wanke kafa har Landan don ganawa da Atiku amma ya ki sauraronsa don sun hada baki da wasu 'yan jam'iyyar
  • Wike ya sanar da cewa, Gwamna Babangida Aliyu ya amsa cewa hada baki suka yi kan cewa ba zasu yi aiki da Jonathan ba

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ya tuno yadda 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Saraki suka yi fatali da rokon tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na hakuri kan hukuncin barin jam’iyyar a 2014.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Wike ya ce gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tanbuwal yana cikin wadanda suka wulakanta Jonathan bayan taron gangamin 2014 da suka dage kan cewa wannan lokaci ne na arewa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

Gwamna Wike
Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya ce kundin tsarin mulkin jam’iyyar na kunshe da tanade-tanade na shiyyoyi kan mukaman zabe da na jam’iyya inda ya koka da yadda wasu ke yin duk abin da za su iya domin yin magudia tsarin.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Za a yi shiyyar jam’iyya da kujerun mukami. A bayyane suka babu shubuha. Amma a kodayaushe mutane za su yi ƙoƙarin yin amfani da tsarin don amfanar kansu.
“Suna ba da labari ta yadda za su yaudari jama’a. Iyayen da suka kafa kasar nan sun san sarkakiyar kasar nan. Sun yi komai ta hanyar da ba su da matsala.
“Kada mutane su manta da tarihi. A 2013 da 2014, akwai batun 'dan takarar shugaban kasa. Jonathan ya fito, Atiku da sauran su sun fice. Tambuwal da tsohon shugaban majalisar dattawa duk sun yi hakan.
“Jonathan ya yi duk abin da zai yi don magance matsala da su. Amma sun yi burus da shi a matsayinsa shugaban kasa mai ci. Shugaban kasar ya tafi Landan domin ganin Atiku, amma ya ki ganawa da shi. Tsohon Gwamna Babangida Aliyu ya yarda cewa duk sun amince ba zasu yi aiki da Jonathan ba."

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Rikicin PDP: "Dole Ayu Ya Yi Murabus" Karin Wasu Jiga-Jigai Sun Yaudari Atiku, Sun Koma Bayan Wike

A wani labari na daban, kungiyar masu ruwa da tsaki na PDP a kudu maso yamma sun ce shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu, zai zama jarumi idan yayi murabus da kansa don samun zaman lafiya da nasarar jam’iyyar a zabe.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta tuna cewa jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici bayan Alhaji Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

Wasu gwamnonin PDP da jiga-jigan jam’iyyar musamman daga yankin kudancin Najeriya sun ce lallai idan ana son yin adalci babu yadda za a yi yankin arewacin kasar ya rike tikitin shugaban kasa da kuma mukamin shugaban jam’iyya na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng