Rikicin PDP: Su Dakatar Da Ni Idan Za Su Iya, Wike Ya Yi Wa PDP Barazana

Rikicin PDP: Su Dakatar Da Ni Idan Za Su Iya, Wike Ya Yi Wa PDP Barazana

  • Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike na jihar Rivers ya fada wa jam'iyyarsa ta PDP a dakatar da shi idan za ta iya
  • Jigon na jamiyar hamayyar ya bayyana hakan ne yayin hira da ya yi da manema labarai a ranar Juma'a, 23 ga watan Satumba a Port Harcourt
  • Wike y ce jam'iyyar ta san abin da zai iya aikata idan har ta ce za ta dakatar da shi idan ta zarge shi da wani abin da bai aikata ba

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers, ya yi wa shugabannin PDP barazana ya ce su dakatar da shi kuma su shirya girben abin da zai biyo baya, The Punch ta rahoto.

Wike ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi a Port Harcourt, yana cewa jam'iyyar ta san abin da zai iya idan ta yi hakan.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Nyesom Wike
Ku Dakatar Da Ni Idan Za Ku Iya, Wike Ya Yi Wa PDP Barazana. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yana amsa tambayar da aka masa ne na cewa duba da irin yadda yan wasu jam'iyyun suka rika ziyartarsa ko hakan na iya zama cin amanar jam'iyyarsa.

Duk 'da da ya ce iyayensa ba za su yi barci ba, shma ba zai yi barci ba - Wike

Gwamnan ya bayyana kansa a matsayin 'abu mai daraja', hakan yasa yan siyasa daga jam'iyyu da dama ke ziyartarsa.

Wike ya ce:

"Ina kira gare su su yi hakan. Sun san abin da zan iya yi. Duk dan da ya ce mahaifinsa ba zai yi barci ba, shima ba zai yi barci ba.
"Idan kai kana da daraja mutane za su rika zuwa wurin ka. Wacce kyakyawan yarinya ne mutane ba su son mata magana?".

Idan Ayu a son PDP ta ci zabe ya cika alkawarin da ya yi na murabus - Wike

Kara karanta wannan

Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014

Ya bayyana cewa idan shugaban jam'iyyar na kasa yana son jam'iyyar ta ci zabe, ya cika alkawarin da ya dauka, ya sauka dan kudu ya gaji kujerarsa.

Ya ce:

"Idan Ayu yana kaunar jam'iyyar kuma yana son ta ci zabe, ya cika alkawarin da ya dauka ya yi murabus.
"Na ji wai idan PDP ta ci zabe, shugaban jam'iyyar na kasa yana son ya zama sakataren gwamnatin tarayya. Wani kuma yana son ya zama shugaban majaliar tarayya.
"Sun raba mukamai. Sun matsa wa shugaban BoT ya yi murabus. Me yasa ba su tursasa wa shugaban jam'iyya na kasa ya yi murabus ba?."

Wike Ya Fara Fallasa, Ya Bayyana 'Makircin' Da Ayu Ya Kitsa Yayin Zaben Fidda Gwanin PDP

A wani rahoto, Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya yi ikirarin cewa shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya yi masa zagon kasa don kada ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan Tsame Hannu Daga Kamfen Atiku, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Yuwuwar Fice Wa Daga PDP

Mr Ayu, kamar yadda ya yi ikirari, ya yi kira ga yan takarar shugaban kasa da dam su janye wa Atiku, wanda daga bisani ya yi nasara, The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel