Wike Ya Fara Fallasa, Ya Bayyana 'Makircin' Da Ayu Ya Kitsa Yayin Zaben Fidda Gwanin PDP

Wike Ya Fara Fallasa, Ya Bayyana 'Makircin' Da Ayu Ya Kitsa Yayin Zaben Fidda Gwanin PDP

  • Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers ya zargi Sanata Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na kasa da shirya makarcin ganin bai ci zaben fidda gwani ba na zaben 2023
  • Wike, a hirar da ya yi da yan jarida a ranar Juma'a ya ce Ayu ya rika bin wasu cikin yan takarar tikitin shugaban kasar na PDP yana cewa su janye wa Atiku don ya kada shi
  • Jigon na jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party ya yi ikirarin cewa Ayu ya sha alwashin zai yi murabus idan shi ne ya lashe zaben cikin gidan na PDP

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya yi ikirarin cewa shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya yi masa zagon kasa don kada ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Mr Ayu, kamar yadda ya yi ikirari, ya yi kira ga yan takarar shugaban kasa da dam su janye wa Atiku, wanda daga bisani ya yi nasara, The Nation ta rahoto.

Wike da Sanata Ayu
Wike Ya Fara Fallasa, Ya Bayyana 'Makircin' Da Ayu Ya Kitsa Yayin Zaben Fidda Gwanin PDP. Hoto: The Nation News.
Asali: Facebook

Ya ambaci wasu cikin wadanda ya ce an tuntube su da su janye wa Atiku kamar Gwamnan Bauchi Bala Mohammed; takwararsa na Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban majalisar tarayya, Sanata Bukola Saraki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ayu ya yi barazanar zai yi murabus idan a zama dan takarar PDP - Wike

Ya yi ikirarin cewa Mr Ayu, kuma ya i barazanar zai yi murabus idan shi ya zama dan takarar shugaban kasa, yana mai cewa shugaban jam'iyyar na kasa ya 'murde' zaben don ganin Mr Atiku ya yi nasara.

2023: Gwamnan PDP Ya Bayyana Matsayin Jam'iyyar Kan Janyewar Wike Da Mutanensa Daga Takarar Atiku

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP Mai Karfin Fada A Ji Ya Bayyana Matsayin Jam'iyyar Janyewar Wike Da Mutanensa Daga Takarar Atiku

A bangare guda, Shugaban kungiyar yakin neman zaben takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Udom Emmanuel, ya jadada bukatar da ke akwai na mutane su rika cika alkawarin su.

Gwamnan na Jihar Akwa Ibom ya yi wannan kiran ne yayin da ya ke martani kan janyewar mutanen Gwamna Nyesom Wike daga kwamitin kamfen din na PDP, Rivers Mirror ta rahoto.

Bangaren Wike na bukatar shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya yi murabus kuma a bawa kudu kujerar shugabancin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel