Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu

  • Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC ya gana da limaman addinin Kirista na arewacin Najeriya
  • Ya bayyanawa manyan limaman cewa, bai zabi Shettima don ware Kirista ba, yayi hakan ne bisa ga cancanta
  • Sai dai bayan kammala taron, limaman sun bayyana cewa ganawar ba tana nufin sun amince tare da goyon bayan Tinubu bane

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu malaman addinin Kirista a karkashin inuwar kungiyar Pentecostal Bishops Forum of Northern Nigeria.

A ganawar da suka yi, Tinubu ya bayyana cewa zabin da ya yi na tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ba barazana ce ga al’ummar Kirista ba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wike: Yadda Atiku, Saraki, Tambuwal, Aliyu, Suka Ki Amincewa da Rokon Jonathan a 2014

Tinubu da Bishops
Tinubu Ya Gana da Limaman Kiristoci, Yace Zabar Shettima ba Barazana bace Garesu. Hoto daga vanguardngr.news
Asali: UGC

Ya kara da cewa, ya yanke shawararsa ne bisa cancanta ba wai addini ba inda ya kara da cewa cancanta ne kawai za ta iya magance kalubalen siyasa da zamantakewar al’ummar Najeriya.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya ce shi abokin al’ummar Kirista ne, don haka ya kamata a yi la’akari da shi ta hanyar tarihi, tsare-tsare da kuma tsarikan ci gaban Nijeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yaya Najeriya za ta ci gaba? Ta yaya za mu kore yunwa? Ta yaya za mu inganta tsaro da kawar da kashe-kashen juna, zubar da jinin ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, shi ne abin da ya kamata mu kai ofis ba addininmu ba.
“Niyyata a fili take, ba addini ba. Niyyata ita ce in ga ci gaban kasar nan, in kawo ci gaba a kasarmu kuma ina da cancanta, mafi kyawun tarihi, mafi kyawun gani, hangen nesa fiye da kowane abokin hamayya.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

“Lokacin da sunayen da aka tantance suka zo, na kalli jaruman wadanda ke cikin jerin sunayen, tarihinsu da komai kwatsam sai ga Kashim Shettima, wanda yake da hazaka, mai jajircewa, wanda a lokacin rikicin Borno ya kare Kiristoci."

- Yace.

Limaman addinin Kiristan sun ce taron ba yana bada tabbacin cewa za su amince da dan takarar APC din bane.

Shugaban kungiyar Pentecostal na Arewacin Najeriya, Archbishop John Praise, ya ce:

"Ba mu kuduri aniyar amincewa da kowa ba, amma ku tambayi lamirinku kuma daga abin da kuka ji da kuma bayanin da shi (Tinubu) ya ba mu. ku yi wa kanku hukuncin wa zai fi yin mulki da tafiyar da kasar nan yadda ya dace.

Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, yayi kira ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da mabiyansa da su dawo a yi kamfen din Atiku da su don zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bayyana Wadanda Za Su Tafiyar Da Gwamnatin Tinubu Idan Aka Zabe Shi

Ayu wanda ya sanar da hakan ta bakin hadiminsa na musamman na yada labarai, Simon Imobo-Tswam, bayan tsagin Wike ya janye daga tawagar kamfen din Atiku saboda Ayu ya ki yin murabus, jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng