Jerin Gwamnoni 8 da suka taba rike kujerar Shugaban Gwamnoni daga 1999 zuwa 2022

Jerin Gwamnoni 8 da suka taba rike kujerar Shugaban Gwamnoni daga 1999 zuwa 2022

  • A tarihin kungiyar Gwamnonin jihohin Najeriya, an samu shugabanni takwas a cikin shekaru fiye da 20
  • Gwamnan farko da ya rike shugabancin kungiyar NGF shi ne tsohon Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu
  • A lokacin Goodluck Jonathan ne aka yi rikicin shugabanci a NGF tsakanin Jonah Jang da Rotimi Amaechi

Abuja - Sai bayan shekarar 1999 aka taba jin kungiyar NGF ta gwamnonin jihohi a Najeriya. Daga 2009 ne kungiyar tayi karfi, har ta shahara sosai.

Kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta, tsakanin 1999 da 2008, aikin kungiyar bai wuce karbar kudin shekara-shekara domin kula da sakatariya.

Bayan rantsar da gwamnoni a Mayun 1999, Abdullahi Adamu ne ya zama shugaban NGF, bai sauka daga kan wannan kujera ba sai a shekarar 2004.

Da Abubakar Bukola Saraki ya karbi rikon NGF, ya kawo sauye-sauyen da ake gani a yau. Da ya bar ofis, sai Rotimi Chibuike Amaechi ya karbe shi.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Jerin Gwamnoni
Gwamnoni a taron NGF Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Su wanene suka rike NGF?

Gwamnonin jihohin Nasarawa, Akwa Ibom, Edo, Kwara, Ribas, Zamfara, Ekiti da Sokoto suka rike wannan kujera a tsawon shekaru 23 da aka yi.

Wanda ya fi kowa dadewa a kan wannan kujera shi ne Abdullahi Adamu wanda yayi shekaru biyar. Luck Igbinedion kuwa shekara daya kacal ya yi.

Legit.ng ta kawo jerin wadanda suka taba shugabantar kungiyar gwamnonin daga 1999 zuwa yau.

1. Abdullahi Adamu Daga 1999 zuwa 2004

2. Arc. Victor Bassye Attah Daga 2004 zuwa 2006

3. Lucky Nosakhar Igbinedion Daga 2006 zuwa 2007

4. Dr. Abubakar Bukola Saraki Daga 2007 zuwa 2011

5. Rotimi Chibuike Amaechi Daga 2011 zuwa 2015

6. Alhaji Abdulaziz Yari Daga 2015 zuwa 2019

7. Dr. Kayode Fayemi Daga 2019 zuwa 2022

8. Aminu Waziri Tambuwal Daga 2022....

Rikici tsakanin Gwamnoni

A shekarar 2011, an samu sabani a kungiyar NGF inda fadar shugaban kasa ta goyi bayan Jonah Jang, duk da gwamnoni sun zabi Rotimi Amaechi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal ya karbe mukamin shugaban gwamnonin Najeriya

Peter Obi shi ne Gwamnan da ya fara zama mataimakin shugaba a tarihin kungiyar ta NGF. Kujerar nan tana zagayawa ne tsakanin Arewa da Kudu.

Kusan tun nan ba a samu wata rigima a NGF ba domin ba a kawo maganar jam'iyya.

Tambuwal ya gaji Fayemi

A ranar Alhamis ne aka ji shugaban kungiyar Peoples Democratic Party Governors Forum (PDP-GF) ya zama sabon gwamnan gwamnonin kasar nan.

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya maye gurbin takwaransa na Ekiti, Kayode Fayemi wanda wa'adinsa na biyu a kan mulki ya zo karshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng