Kasar Burtaniya Ba Zata Sa Baki A Zaben Najeriya Ba A 2023, Inji Wakiliyar Burtaniya
- Burtaniya ta bayyana matsayarta game da zaben 2023 mai zuwa nan ba da jimawa, ta fadi abin da za ta yi
- Wakiliyar Burtaniya a Najeriya ta kai ziyara jihar Kebbi, ta bayyana irin jin dadin da ta ji da ganin kyawun jihar
- Burtaniya ta yi godiya ga dukkan 'yan Najeriyan da suka mika sakon ta'aziyyar mutuwar sarauniya Elizabeth II
Birnin Kebbi - Kasar Burtaniya ta ba 'yan Najeriya tabbacin cewa, ba za ta tsoma baki a lamurran zaben 2023 mai zuwa nan kusa ba.
Babbar Kwamishinira Burtaniya a Najeriya, Ms Catriona Laing ce ta bayyana hakan, inda tace Burtaniya za ta tsaya tsaka-tsaki a lokacin zabukan.
Ta bayyana haka ne a Birnin Kebbi ta jihar Kebbi a wata tattaunawa da manema labarai, jaridar Leadership ta ruwaito.
Ta ce abin da Burtaniya ke sa ido a kai ba komai bane face zabe na adalci da gaskiya da zai kai ga mika mulki ga wanda ya dace.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta kuma bayyana cewa, Burtaniya na kaunar dimokradiyya, kuma tana jin dadin yadda ake dimokradiyya a kasashen duniya, duk da cewa tsarin mulkin na samun tasgaro a wasu kasashen Afrika.
Za mu ba da hadin kai wajen kawo shugaba nagari a Najeriya
A bangare guda, ta ce Burtaniya za ta hada kai da Najeriya tare da ba da gudunmawar da ake bukata wajen domin marawa wanda aka zaba a 2023 baya.
Ta shaidawa manema labarai cewa, wannan ne zuwanta na farko jihar Kebbi, kuma ta yi farin ciki da ganin ayyukan ci gaba da gwamna Atiku Bagudu ya yi.
Ta kara da cewa, da yadda ta ga jihar Kebbi, Burtaniya za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar tare da zuba hannun jari a wasu bangarori.
Daga karshe ta godewa 'yan Najeriya baki daya da suka yi ta'aziyyar mutuwar sarauniya Elizabeth II da kuma taya sarki Charles III murnan samun hawa kujerar da ya dade yana jira.
Ina da Dangantaka Mai Karfi da Sarauniyar Ingila Elizabeth II, Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo
A wani labarin, a yayin da ake ci gaba da jigilar binne sarauniyar Ingila Elizabeth II, tsohon shugaban kasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi wata magana mai daukar hankali.
Obansaji ya ce yana alaka da dangantaka mai karfi da sarauniya Elizabeth II, inda yace yana mata fatan alheri kuma yana matukar girmama ta, Daily Trust ta ruwaito.
A wata sanarwa da Obasanjo ya fitar ta hannun hadiminsa, Kehinde Akinyemi, ya ce sarauniya na da halin dattaku da iya zama da mutane, kuma shi kansa yana kyakkyawar dangantaka ita.
Asali: Legit.ng