Rikicin PDP: "Sun Ci Amanar Jonathan, Yanzu Abin Ya Dawo Kansu", FFK Ya Ragargaji Atiku, Saraki Da Tambuwal
- Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya ya ragargaji Atiku, Saraki da Tambuwal kan rikicin jam'iyyar PDP
- Tsohon jigon na jam'iyyar PDP da a yanzu ya dawo APC ya ce kusan dukkan mutanen da ke bangaren Atiku sun ci amanar Goodluck Jonathan a zaben 2023
- Fani-Kayode ya yi nuni da cewa abin da ke faruwa da Atiku Abubakar dan takarar na PDP sakayya bisa cin amanar da suka yi wa tsohon shugaban kasa Jonathan a 2015
Facebook - A yayin da ake cigaba da rikici tsakanin shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Mr Femi Fani Kayode, tsohon jigon jam'iyyar da yanzu ya koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin.
A cewar wani rubutu da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook, Mr Fani-Kayode ya zargi dan takarar shugaban kasar PDP, Atiku Abubakar, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, da Sanata Bukola Saraki da cin amanar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rubutun da ya yi ta ce:
"Abu daya da zan ce game da tawagar Wike a PDP shine kowanne cikinsu ya tsaye tare da GEJ a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.
"Akasin haka, dukkan masu ruwa da tsaki da ke bayan bangaren ciki har da Atiku, Tambuwal da Saraki sun ci amanar GEJ a zaben 2015.
"Duk abin da ka shuka shi zaka girba."
APC Ta Shiga Tasku A Rivers, Wike Ya Tarbi Daruruwan Mambobinta Da Suka Dawo PDP
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers a ranar Asabar ya tarbi daruruwan mambobin APC da suka shigo PDP, rahoton Channels TV.
Wadanda suka hallarci taron sun da aka yi a Port Harcourt, sun hada da shugaban PDP na Jihar Rivers, Mr Desmond Akawor; tsohon mamba na kwamitin amintattu na APC, Mr Sam-Sam Jaja; tsohon kwamishinan wasanni, Mr Fred Igwe; da daruruwan magoya bayansu.
Sauran wadanda suka shigo PDPn sune Mr Sylver Opusunju, Mr Tele Bethram Ikuru, Mr Princewill D*ke, Mr Reginald Onwuka, Mr Bestman Amadi, Mr Amadi Nnokam, Mr Muma Gift da Mr Kennedy Ebeku.
Asali: Legit.ng