APC Ta Shiga Tasku A Rivers, Wike Ya Tarbi Daruruwan Mambobinta Da Suka Dawo PDP

APC Ta Shiga Tasku A Rivers, Wike Ya Tarbi Daruruwan Mambobinta Da Suka Dawo PDP

  • Daruruwan mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sun bar jam'iyyarsu sun koma jam'iyyar PDP a Jihar Rivers
  • Gwamna Wike na Jihar Rivers shine ya tarbe su a ranar Asabar ya kuma sanar da su cewa sun sauya sheka lokacin da ya dace
  • Daga cikin wadanda suka sauya shekan akwai Sylver Opusunju, Tele Bethram Ikuru, Princewill D*ke, Reginald Onwuka, Bestman Amadi dss

Jihar Rivers - Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers a ranar Asabar ya tarbi daruruwan mambobin APC da suka shigo PDP, rahoton Channels TV.

Wadanda suka hallarci taron sun da aka yi a Port Harcourt, sun hada da shugaban PDP na Jihar Rivers, Desmond Akawor; tsohon mamba na kwamitin amintattu na APC, Sam-Sam Jaja; tsohon kwamishinan wasanni, Fred Igwe; da daruruwan magoya bayansu.

Kara karanta wannan

Hotuna sun ba da mamaki yayin da Sarkin Musulmi ya gana da wani gwamnan Kudu

Yan PDP da suka koma PDP a Rivers.
Wike Ya Karbi Daruruwan Yan APC Da Suka Shigo PDP A Rivers. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

Sauran wadanda suka shigo PDPn sune Sylver Opusunju, Tele Bethram Ikuru, Princewill D*ke, Reginald Onwuka, Bestman Amadi, Amadi Nnokam, Muma Gift da Kennedy Ebeku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar gwamnan, aikin da ke gabansa shine ya tabbatar dukkan yan takarar Rivers sun ci zabe a shekara mai zuwa.

Wike ya ce:

"Jihar Rivers na da muhimmanci a wuri na fiye da wani mutum ko wata kungiya.
"Dukkan ku da kuka dawo cikin iyalan ku, kuna da rawar da za ku taka don ganin dan takarar gwamnan mu ya yi nasara."

Gwamnan ya ce wadanda suka shigo PDPn sun sauya sheka a lokacin da ya dace, yana mai cewa zaben 2023 ba na 'manyan mutane bane, ba na wanda suka ki dawowa gida su tattara kan al'umma bane; kawai siyasarsu a waje ne.'

Ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Wike da Jerin Sauran Masu Harin Shugaban Kasa da Suka Ki Yin Zama da Atiku

"A gida ake gina yan siyasa. Na canja tsarin na a wannan zaben - babu manyan mutane, zan yi aiki ne da wadanda ke da muhimmanci a kowanne yanki.
"Duk wadanda suke dawowa ba ka jin sunansu amma sune mutanen da ke aiki. Don haka, su muke dawo da su kuma masu kiran kansu manyan mutane suna firgita."

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

A wani rahoton, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.

Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.

Amma, Wike cikin sanarwar da kakakinsa, Kelvin Ebiri ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana kalaman da aka danganta da Lamido a matsayin abin kyama da raini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel