Wike Ya Rasa Ƙashin-Baya a Rikicin PDP, Na Hannun Damansa Yace Atiku Zai Yi Wa Aiki

Wike Ya Rasa Ƙashin-Baya a Rikicin PDP, Na Hannun Damansa Yace Atiku Zai Yi Wa Aiki

  • Ayodele Peter Fayose ya sake nanata cewa babu abin da zai sa ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC
  • Tsohon gwamnan na jihar Ekiti ya roki a ajiye makaman yakin da ake yi a PDP domin a doke APC a 2023
  • Fayose yace burinsa shi ne ‘yan takaran jam’iyyar PDP suyi nasara a zabe mai zuwa a kowane mataki

Lagos - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, yace duk da sabanin da ake yi da su a PDP, ba zai sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC ba.

Premium TImes ta rahoto Ayodele Peter Fayose yana cewa yana tare da Gwamna Nyesom Wike a rikicinsa da ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar.

Duk da bambancinsu da Atiku Abubakar, tsohon gwamnan yace zai mara baya ne ga ‘dan takaran shugaban kasan da duk wani wanda PDP ta tsaida.

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

Ayo Fayose ya yi wannan bayani da ya zanta da wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP a garin Ado Ekiti a ranar Litinin, 19 ga watan Satumba 2022.

Atiku/Okowa: Ba mu da ja - Fayose

Fayose wanda ya yi gwamna sau biyu a Ekiti yake cewa ya yarda Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa ne ‘yan takarar shugabancin kasa a inuwar PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan siyasar yace zai so kowane ‘dan takaran PDP ya samu nasara a 2023, daga ciki har da ‘dan da ya haifa wanda yake harin kujerar majalisar tarayya.

Wike .
Manyan PDP, Atiku da Wike a Abuja Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Ina nan a PDP inji Fayose

“An fadi abubuwa da yawa, amma kamar yadda na fada sau da yawa, bari in sake fada a nan, ba zan taba shiga APC a kan kowane dalili ba.”
“A duk wadannan abubuwa da muke samu a jam’iyya, babu wanda yace Atiku Abubakar da Dr. Ifeanyi Okowa ba ‘yan takaranmu ba ne.”

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Yi Wa Peter Obi Tsirara, Ya Tona Gazawarsa a Lokacin Yana Mulki

“Muna da ‘yan takaran Sanata, majalisar wakilan tarayya da majalisun dokoki a nan. Daga ciki har da ‘dan cikina, Joju da sauran yarana a siyasa.
Abin da nake so, shi ne su lashe zaben da za ayi.”

- Ayi Fayose

Punch tace a jawabinsa, Fayose ya roki wadanda aka batawa rai a jam’iyyar PDP suyi hakuri a lashe zabe tukuna, yace bayan 2023 sai a cigaba da rigingimun.

Shugaban PDP na rikon kwarya a jihar Ekiti ya yi magana a madadin kwamitin SWC. Shi ma Bisi Kolawole ya yi amfani da damar, ya ce wani abin a taron.

Tinubu ya ba Rotimi Akeredolu aiki

Dazu ne muka samu labari Asiwaju Bola Tinubu ya kinkimo wanda zai yi masa Sarkin yakin neman takara a yankin Yarbawa a zaben Shugabancin kasa.

Tinubu ya bayyana dalilinsa na dauko Gwamna Rotimi Akeredolu wanda shi ne shugaban gwamnonin Kudu ta yamma, yace ya nuna kwarewa a siyasa.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Hadimin Gwamnan Kaduna da Mambobin APC Sama da 13,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel