Gwamna Wike Ya Kira Taron Masu Ruwa da Tsaki Na Jam'iyyar PDP a Ribas

Gwamna Wike Ya Kira Taron Masu Ruwa da Tsaki Na Jam'iyyar PDP a Ribas

  • A karon farko tun bayan shan kaye hannun Atiku a watan Mayu, Gwamna Wike ya kira taron masu ruwa da tsaki na PDP a jihar Ribas
  • Wata majiya tace duk da ba'a faɗi ajendar da za'a tattauna ba amma taron ba zai rasa nasaba da rikicin PDP a matakin kasa ba
  • A gobe Jumu'a 23 ga watan Satumba, 2022, gwamna Wike zai yi jawabi a gidan gwamnatinsa dake Patakwal

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kira taron shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP reshen jiharsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wannan taron zai zama na farko na gwamna ya kira a jihar tun bayan kammala zaɓen fidda gwani na takarar shugaban kasa a watan Mayu.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Gwamna Wike Ya Kira Taron Masu Ruwa da Tsaki Na Jam'iyyar PDP a Ribas Hoto: Nyesom Wike/facebook
Asali: Facebook

Duk da dai ba'a san makasudin kiran taron ba, wata majiya tace duk abubuwan dake faruwa a jam'iyyar PDP a matakin ƙasa masu ruwa da tsaki a jihar ba su ji ta bakin gwamnan ba kai tsaye har yanzu.

Kara karanta wannan

Komai Ya Dagule, Nan Ba da Jimawa Ba Zamu Haɗa Kan Atiku da Wike, Shugaban BoT-PDP

Bisa haka, ana tsammanin jiga-jigan zasu ji kai tsaye daga bakin Wike matsayar da ya ɗauka da kuma mataki na gaba da zasu bi game da rikicin da ya hana PDP rawar gaban hantsi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda ake tsammanin zasu halarci taron

Mutanen da ake kayutata zaton za su halarci taron sun haɗa ɗa baki ɗaya mambobin majalisar zartarwan jam'iyya na jihar, shugabannin PDP a matakin kananan hukumomi da wasu jiga-jigai da aka zaɓa.

Majiyar da muka samu tace taron yana da alaƙa da rikicin baya-bayan nan dake faruwa a PDP yayin da ake tsammanin Wike zai yi wa mutanensa bayanin matsayar tawagarsa na tsame hannu daga majalisar kamfe.

Wannan na zuwa ne gabanin taron manema labarai da aka tsara gudanarwa ranar Jumu'a 23 ga watan Satumba, 2022 da safe, wanda gwamnan da kansa zai yi jawabi a gidan gwamnati da ke Patakwal.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Atiku ya ce ba zai iya tilastawa shugaban PDP ya ajiye mukaminsa ba

An yi amanna cewa Wike zai yi dogon fashin baki game da matsalar dake tsakaninsa da ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, musamman kan kalaman Atiku na ranar Laraba.

Idan baku manta ba Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa yayin martani kan matsayin 'yan tawagar Wike, Atiku yace ba wanda ya isa ya tilasta wa Ayu ya yi murabus.

A wani Labarin kuma Gwamnan Arewa Ya Bayyana Wadanda Za Su Tafiyar Da Gwamnatin Tinubu Idan Aka Zabe Shi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa gwamnatin dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu za ta cika da matasa idan aka zabe shi.

Gwamnan ya bayyana cewa Tinubu zai zabo kwararru da gogaggu ne kawai, amma matasa ne za su tafiyar da harkokin gwamnatin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262