Rikicin PDP: "Dole Ayu Ya Yi Murabus" Karin Wasu Jiga-Jigai Sun Yaudari Atiku, Sun Koma Bayan Wike

Rikicin PDP: "Dole Ayu Ya Yi Murabus" Karin Wasu Jiga-Jigai Sun Yaudari Atiku, Sun Koma Bayan Wike

  • An samu karin mutane a jam'iyyar PDP da ke kira ga lallai sai shugaban jam'iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu, ya yi murabus
  • Kungiyar masu ruwa da tsaki na PDP a kudu maso yamma ta ce yakamata Ayu ya sadaukarwa Atiku don ya lashe zaben 2023
  • Ta ce ta hanyar murabus din shugaban jam'iyyar ne za a samu zaman lafiya har a kai ga lashe zabukan da ke tunkarowa

Kungiyar masu ruwa da tsaki na PDP a kudu maso yamma sun ce shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu, zai zama jarumi idan yayi murabus da kansa don samun zaman lafiya da nasarar jam’iyyar a zabe.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta tuna cewa jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici bayan Alhaji Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

Shugaban APC na kasa
Rikicin PDP: "Dole Ayu Ya Yi Murabus" Karin Wasu Jiga-Jigai Sun Yaudari Atiku, Sun Koma Bayan Wike Hoto: @iyorchiaayu
Asali: Twitter

Wasu gwamnonin PDP da jiga-jigan jam’iyyar musamman daga yankin kudancin Najeriya sun ce lallai idan ana son yin adalci babu yadda za a yi yankin arewacin kasar ya rike tikitin shugaban kasa da kuma mukamin shugaban jam’iyya na kasa.

Masu jagorantar fafutukar ganin Ayu wanda ya fito daga arewa ta tsakiya ya yi murabus, sune Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da wasu shugabannin jam’iyyar daga kudancin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika, a ranar 17 ga watan Satumba, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da wasu shugabannin PDP a kudu maso yamma sun yi kira ga murabus din Ayu a taron masu ruwa da tsaki na yankin da suka yi da Atiku.

A wata sanarwa dauke da sa hannun shugabannin kungiyar, Banji Okunomo da Gani Taofik a Lagas a ranar Alhamis, kungiyar ta nuna goyon bayanta ga kira da ake yi na shugaban jam’iyyar yayi murabus, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

A cewarta, murabus din shugaban jam’iyyar shine hanya daya da za a samu zaman lafiya a jam’iyyar.

Kungiyar ta bayyana cewa yakamata Ayu ya sadaukar wa Atiku don ya lashe zabe mai zuwa.

Ta bukaci Atiku da yayi taka-tsan-tsan da mugun shawarwari daga wasu bara-gurbi a jam’iyyar.

Har ila yau, ta bayyana cewa bara gurbin na bayar da shawarwarin da ka iya kawo cikas ga damar da Allah ya budewa PDP a zaben da ke tafe.

Ta ce:

“Shakka babu yan Najeriya na jiran PDP a matsayin madadin gwamnati, kuma Allah ya kiyaye, idan wannan dama ta wuce mu, ‘yan Najeriya ba za su sake hulda da PDP ba.’
"Muna kira da a gaggauta dawo da kwarin gwiwa hadin kai a cikin Jam'iyyar.”

Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

A wani labarin, Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, yayi kira ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da mabiyansa da su dawo a yi kamfen din Atiku da su don zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnoni, tsaffin ministoci, jiga-jigai masu goyon bayan Wike sun yi hannun riga da kwamitin kamfen PDP

Ayu wanda ya sanar da hakan ta bakin hadiminsa na musamman na yada labarai, Simon Imobo-Tswam, bayan tsagin Wike ya janye daga tawagar kamfen din Atiku saboda Ayu ya ki yin murabus, jaridar Punch ta rahoto.

Tsagin Wike sun jaddada cewa, mukamin shugaban jam'iyya na kasa ya zama dole ya kasance a kudancin kasa nan domin a samu daidaito da adalci tunda arewa ta samu tikitin takarar shugabancin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng