Zaben 2023: Kada Ku Dinga Mana Kallon Marasa Amfani, Mambobi 16m Garemu, Kungiyar Masu Nakasa

Zaben 2023: Kada Ku Dinga Mana Kallon Marasa Amfani, Mambobi 16m Garemu, Kungiyar Masu Nakasa

  • Nakasassu a Najeriya sun kai kusan kashi 25 cikin 100 na daukacin al'ummar kasar bisa ga kididdigar baya-bayan nan
  • Da yake magana a madadin nakasassu a Najeriya, gidauniyar zabiyoyi ta baiwa jam’iyyun siyasa shawarar gudanar da yakin neman zabe tare da hadawa da su
  • A ranar Laraba 28 ga watan Satumba ne za a fara yakin neman zabe a kasar nan kamar yadda sashi na 94(1) na dokar zabe ta 2022 ta tanada

Ambasada Jake Epelle, wanda ya kafa gidauniyar zabiyoyi, ya shawarci ‘yan takara da jam’iyyun siyasa a babban zabe mai zuwa na 2023 da su tabbatar da sanya su yayin gudanar da yakin neman zabe.

Epelle ya gargadi jam’iyyu da kada su dauki kuri’un nakasassu miliyan 16 a kasar nan a banza, ya kara da cewa nakasassu na da adadin da za su iya sauya sakamakon zabe a matakai daban-daban.

Kara karanta wannan

UNGA77: Shugaba Buhari Yayi Bankwana da Shugabannin Kasashen Duniya

Albino Foundation
Zaben 2023: Kada Ku Dinga Mana Kallon Marasa Amfani, Mambobi 16m Garemu, Kungiyar Masu Nakasa. Hoto daga @TAF_Nig
Asali: Twitter

Yace a tabbatar da cewa kayan kamfen sun kasance yadda zasu iya kai wa nakasassun kasar nan, masu matsalar gani da zabiyoyi da sauransu.

Kamar yadda yake kunshe a dokokin masu nakasa na 2018, jam'iyyun siyasa su tabbatar da wuraren kamfen da taruka duk zasu zama masu saukin halarta har da ofisoshin jam'iyyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa, al'ummar nakasassu ba zata hakura ba wurin mika bukatar bayar da ayyuka ga mambobinta daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.

A yayin yabawa kokarin hukumar zaben mai zaman kanta, INEC, wurin tabbatar da cewa masu nakasa sun shiga tsarin zabe, Epelle yayi kira ga jam'iyyun siyasa da su goyi bayan hakan inda yace:

"Domin tabbatar da gasar, akwai matukar amfani idan jam'iyyu suka rungumi tsarin saka al'ummar da basu da wakilci.
"Wannan lamarin zai taimaka wurin ginawa tare da dawwamar da ginshikin wakilci tare da samun yardar 'yan kasa.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

"INEC ta dauka matakan yakice dukkan shingen da ke hana nakasassu zama masu kada kuri'u da matakan da ta sanya domin tabbatar da cewa an saka masu nakasa cikin harkar zabe a kasar nan.
“A yayin yabawa kokarin INEC kan yadda ta janyo mu wurin shiga harkar zabe ta hanyar tsara yadda masu nakasa zasu samu shiga, muna kira ga jam'iyyun siyasa da su runguma tare da inganta hakan ta yadda za ji muryoyinmu a yayin zabe."

Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, yayi kira ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da mabiyansa da su dawo a yi kamfen din Atiku da su don zaman lafiya.

Ayu wanda ya sanar da hakan ta bakin hadiminsa na musamman na yada labarai, Simon Imobo-Tswam, bayan tsagin Wike ya janye daga tawagar kamfen din Atiku saboda Ayu ya ki yin murabus, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Kwamishinan Yan Sanda Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Masu Karya Dokar Zabe A Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel