2023: Kwamishinan Yan Sanda Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Masu Karya Dokar Zabe A Kaduna

2023: Kwamishinan Yan Sanda Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Masu Karya Dokar Zabe A Kaduna

  • Yekini Adio Ayoku, kwamishinan yan sanda na Jihar Kaduna ya gargadi jam'iyyun siyasa, yan takarar da mazu zabe kan karya dokar zabe a 2023
  • Ayoku ya ce rundunar yan sanda za ta kama kuma ta gurfanar da duk wani da aka kama yana karya dokoki zabe yayin babban zabe ba tare da sassauci ba
  • Adio ya yi wannan gargadin ne a lokacin da tawagar kungiyar ya jarida NUJ na Kaduna ta kai masa ziyararban girma a ofsihinsa da ke Kaduna yana mai cewa sun shirya tsaf don zaben

Kaduna - Kwamishinan yan sandan Jihar Kaduna, Yekini Adio Ayoku ya ce rundunarsa ba za ta sassauta wa duk wanda ya karya dokar zabe ba, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

Don haka, ya gargadi jam'iyyun siyasa da yan takararsu su zama masu biyayya ga dokar zabe idan ba haka ba kuma a kama su a tsare su.

Mr Ayoku
Ba Za Mu Sassauta Wa Masu Karya Dokokin Zabe Ba, Kwamishinan Yan Sandan Kaduna. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ayoku ya kuma shawarci iyaye kada su bari a yi amfani da yaransu a matsayin yan daban siyasa kafin, yayin da bayan zabe.

Da ya ke jawabi ga shugabannin kungiyar yan jarida ta Najeriya, NUJ, a Kaduna wadanda suka kai masa ziyarar ban gajiya ofishinsa a ranar Talata, kwamishinan yan sandan ya ce za a samar da tsaro a yayin zaben don haka ba za a samu matsala ba.

Ayoku ya bayyana gamsuwarsa game da kokarin da yan jarida ke yi a jihar, yana mai cewa bai samu labari mara dadi ba game da rundunarsa tun da ya zama kwamishina.

Ya yi kira ga yan jaridan su cigaba da bada hadin kai da goyon baya da suka saba bawa rundunar, ya kara da cewa bai kamata yan jarida su rika kambama masu garkuwa ba yayin wallafa rahotanninsu.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Kai Wuya, Zasu Ba Wasu 'Yan Takara Mamaki A 2023, Gwamna

Ya fada wa yan jaridan:

"Muna alkawarin za mu bada tsaro yadda ya kamata yayin babban zaben 2023. Za mu bada tsaro sosai domin zaben ya tafi lafiya sumul.
"Muna shawartan jam'iyyun siyasa da yan takarar su bi dokokin zabe, kuma za mu dauki mataki ba tare da sasauci ba kan duk wanda ya karya dokar zaben."

Muna bukatar inganta hadin gwiwa da yan sanda - Shugaban NUJ na Kaduna

A wurin taron, shugaban na NUJ, Hajiya Asmau Halilu, ta shaidawa kwamishinan cewa akwai bukatar a inganta hadin gwiwa tsakanin kungiyar da yan sanda ta hanyar bawa yan jaridan bayanai a kan lokaci.

Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

A wai rahoton, tsohon babban jami'in tsaron marigayi Janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha a ranar Asabar, ya zubar da hawaye kan batun rashin tsaro a Najeriya.

Ran dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Action Alliance (AA) ya motsa a lokacin da ya tarbi gamayyar kungiyoyin matan kirista na arewa a gidansa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel