Yanzu-Yanzu: Sanata Shekarau Ya Sanar da Matakin Sauya Sheka a Zaman Majalisar Dattawa

Yanzu-Yanzu: Sanata Shekarau Ya Sanar da Matakin Sauya Sheka a Zaman Majalisar Dattawa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano kuma gwamna mai wakiltan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya koma jam’iyyar PDP
  • Shekarau ya sanar da sauya shekar ne a zauren majalisar dattawa a yau Laraba, 21 ga watan Satumba
  • Kafin sauya shekarsa, Sanatan ya kasance mamba a jam’iyyar New Nigeria Peoples (NNPP) mai kayan marmari

Abuja - Sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a hukumance, jaridar Daily Post ta rahoto.

Shekarau ya sanar da majalisar dattawa matakin sauya shekar nasa ne a yayin zamanta na yau Laraba, 21 ga watan Satumba, jaridar Punch ta rahoto.

Shekarau
Yanzu-Yanzu: Sanata Shekarau Ya Sanar da Matakin Sauya Sheka a Zaman Majalisar Dattawa Hoto: Dailypost.ng
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kasance mamba a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party tasu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kafin sauya shekar tasa.

Da farko dai ya fara komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kafin ya koma NNPP yanzu kuma ya sake komawa PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

A wani labarin kuma, shugaban jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Rufai Ahmed Alkali, ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a matsayin wanda zai zama ‘shugaban kasa mai likimo’.

Ahmed Alkali ya bukaci yan Najeriya da su tabbata basu zabi tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Dan yake martani ga wani hoton Tinubu da ya yadu inda aka gano shi yana bacci a fadar sarkin Gombe a karshen mako, Alkali ya ce NNPP na aiki tukuru domin lashen zaben shugaban kasa na 2023, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel