Ana Shirin Tunkarar 2023, Shugaban APC a Yankin Jihar Ondo Ya Rasu

Ana Shirin Tunkarar 2023, Shugaban APC a Yankin Jihar Ondo Ya Rasu

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Ondo ta gabas a jihar Ondo, Frederick Otemuyiwa, ya kwanta dama
  • Kakakin APC reshen jihar, Mista Alex Kalejaiye, wanda ya sanar da rasuwar, yace sun yi babban rashi ana tsaka da shirin 2023
  • Duk da bai ba da cikakken bayani kan rasuwar ba, yace APC ta miƙa ta'aziyya ga iyalansa da ɗaukacin al'ummar yankinsa

Ondo - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙaramar hukumar Ondo ta gabas a jihar Ondo, kudu maso yammacin Najeriya, Frederick Otemuyiwa, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, mai magana da yawun jam'iyar APC reshen jihar, Mr Alex Kalejaiye, shi ne ya bayyana rasuwar a wata sanarwa da ya fitar yau Talata.

Taswirar jihar Ondo.
Ana Shirin Tunkarar 2023, Shugaban APC a Yankin Jihar Ondo Ya Rasu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai dai kakakin APC, wanda ya nuna baƙin cikinsa da faruwar lamarin, bai ba da cikakken bayani kan sanadiyyar rasuwar marigayin ba.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Kakakin Majalisar Dokokin Jiha Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa, An Naɗa Sabo

Mista Kalejaiye ya bayyana marigayin da mutum mai sadaukarwa kuma jigo, wanda ke iya bakin kokarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan jam'iyya musamman a matakin ƙaramar hukuma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC ta miƙa ta'aziyya

A wani sashin sanarwar, Kakakin APC yace:

"Mamacin mutum ne mai basira mai gina kyakyawar alaƙa a siyasa, wanda ke taka muhimmiyar rawa a tarukan majalisar zartarwan jam'iyya ta jiha."
"Ba ƙaramin rashin sa'a bane tafiyarsa a yanzu da muke bukatar shugabancinsa, kwarewa da salon jawo hankalin mutane yayin da ake tunkarar babban zaɓe na gaba."
"Muna Addu'a Allah ya sa shi a makwanci mai salama kuma muna miƙa ta'aziyya ga iyalansa, mambobin jam'iyyar APC da ɗaukacin al'ummar ƙaramar hukumar Ondo ta gabas."

A wani labarin kuma An Fallasa Shirin Wasu Gwamnonin PDP da Jiga-Jigai Na Goyon Bayan Tinubu a 2023

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Karɓi Ɗaruruwan Masu Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC Ciki Har da Ɗan Takarar Gwamna

Alamu sun nuna cewa wasu gwamnonin PDP na shirin yaudarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban kasa na 2023.

Wasu bayanai da aka tattara sun yi ikirarin cewa akwai wasu gwamnoni da jiga-jigan PDP da ka iya koma wa bayan Tinubu na APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel